Tsohon mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC, Timi Frank, ya yi kira da a saki Omoyele Sowore cikin gaggawa, yana mai bayyana tsare shi a matsayin abin da bai dace ba.

Frank ya kuma buƙaci Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, (DSS) da sauran hukumomin tsaro su karkata hankalinsu wajen magance matsalolin rashin tsaro da suke addabar ƙasa maimakon ci gaba da tsare masu sukar gwamnati.

Yace ya kamata hukumomin tsaro su fi mayar da hankali kan yaƙi da ‘yan ta’adda da masu garkuwa mutane da sauran masu aikata laifuka da ke barazana ga rayyuka da dukiyoyin al’umma a faɗin ƙasar.

Frank ya  ƙara jaddada cewa kare ‘yancin faɗar albarkacin baki da bin doka da oda na da muhimmanci wajen tabbatar da dimokuraɗiyya da adalci a ƙasa.

Ya kuma bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau ranar talata, bayan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya  dake Abuja ta yanke a ranar Litinin, inda ta ba da umarnin a tsare Sowore a gidan gyaran hali na Kuje har sai an saurari buƙatarsa ta ƙalubalantar soke belinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *