Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, ya sake jaddada buƙatar Tarayyar Afirka (AU) ta tattauna batun ƙara samun hare-haren ƙyamar baƙi kan ‘yan ƙasashen Afirka da ke zaune a Afirka ta Kudu.

Mahama ya bayyana hakan ne yayin tattaunawar bangarori biyu da aka gudanar a gefen Babban Taron Gaggawa na Tarayyar Afirka da aka gudanar a Accra.

Ya ce Ghana na kira ga Hukumar Tarayyar Afirka da ta shigar da batun cikin ajandar taron AU na gaba, domin samun damar tattaunawa kan matsalar tare da neman mafita mai ɗorewa.

Shugaban ya bayyana cewa yana maraba da amincewar Shugaban Hukumar AU, Mahmoud Ali Youssouf, na cewa akwai bukatar a gaggauta gabatar da batun domin tattaunawa a taron na gaba.

Mahama ya ce a ganawar da ya yi da wani wakilin musamman da Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya aiko zuwa Accra, ya bayyana matsayin Ghana a fili kan lamarin.

Ya ce Ghana ba ta da wata ƙiyayya ga Afirka ta Kudu, amma tana matuƙar damuwa game da hare-haren da ake kai wa ‘yan ƙasashen waje da kuma asarar dukiya da jari da ‘yan kasashe daban-daban na Afirka suka fuskanta.

A cewar Mahama, irin waɗannan hare-hare suna raunana manufar haɗin kan Afirka da kuma ƙoƙarin da ake yi na samar da haɗin kai a fannin tattalin arziki da zamantakewa a nahiyar.

Ya bayyana cewa yin watsi da matsalar ba zai magance tushen abin da ke haddasa ta ba, shi ya sa Ghana ta rubuta wa Hukumar AU a hukumance domin neman a sanya batun cikin ajandar taron shugabannin ƙasashen Afirka.

Mahama ya ce tattauna batun a ƙarƙashin tsarin AU zai bai wa Afirka ta Kudu damar bayyana matsayinta cikin yanayi mai kyau, tare da bai wa ƙasashen nahiyar damar yin aiki tare wajen samar da mafita.

Ya jaddada cewa ƙarfin nahiyar Afirka yana cikin haɗin kai, yana mai cewa Ghana za ta ci gaba da yin aiki tare da sauran ƙasashe mambobin AU domin kare mutunci, tsaro da kuma jarin ‘yan Afirka a duk inda suke a nahiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *