Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirinsa na kafa kamfanin jirgin saman kasuwanci mallakar jihar domin samar da damar yin aiki ga ‘yan asalin jihar da suka kammala horon tuƙin jirgin sama na ƙwarai.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin Taron Majalisar Zartarwa karo na 40 da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Kano, inda ya karɓi lambobin yabo da dama, ciki har da girmamawa daga Ƙungiyar Matukan Jirgin Sama na Jihar Kano (Kano State Pilot Association) domin amincewa da jajircewarsa wajen tallafa wa mambobin kungiyar su kammala horonsu na harkar jirgin sama.
Wannan ci gaba ya fito ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.
- Gasar cin Kofin Duniyar da ba Najeriya a ciki, ba cikakke ba ne – Shugaban CAF Motsepe
- Arsenal ta sayi Tzolis daga Club Brugge kan fam miliyan 34
- Super Falcons za ta samu dala miliyan 2 idan ta…
Yayin da yake jawabi a taron, Yusuf ya ce ana sa ran kamfanin jirgin saman na Kano (Kano Airline) zai fara gudanar da ayyukansa a cikin shekara guda mai zuwa.
Ya ce”Da yardar Allah, kamfanin jirgin saman Kano da ake shirin kafa zai fara ayyukansa a cikin shekara guda mai zuwa. Muna da cikakken aniyyar ba da duk wani tallafi da ake buƙata domin tabbatar da wannan aiki da kuma nasarar tafiyar da shi,” in ji gwamnan.
Yusuf ya yi wannan shela ne bayan ya karɓi lambobin yabo da dama, har da ta kungiyar matukan jirgi ta jihar Kano saboda tallafin da gwamnatinsa ke ba mambobin su wajen kammala horon harkar rufe fannin sufurin jiragen sama.