Tsohon Ministan Wasanni, Barista Solomon Dalung, ya baiwa Gwamnan Jihar Pilato, Barista Caleb Mutfwang, awanni 72 ya janye kalaman sa, tare da baiwa al’ummar jihar haƙuri.
Matakin ya biyo bayan wasu kalamai da aka jiyo gwamnan na yiwa al’ummar Igbo mazauna jihar, inda ya yi da’awar cewa “an yaudari” mutanen Pilato ne domin shiga Yaƙin Basasa na Najeriya, a shekarar 1967 zuwa 1970.
A martanin da Dalung ya fitar a shafukan sa na sada zumunta, ya bayyana kalaman gwamnan a matsayin jahiltar tarihi da cin fuskar jihar, da magabatan ta suka shiga yaƙin domin tabbatar da haɗin kan ƙasa.
- Dole ne Arewa Maso-Gabas ta fi kowa aiki wajen yaƙar ta’addanci— Tinubu
-
Majalisar Wakilai ta amince da saurarar ƙudirin kafa ’yan sandan Jihohi
Dalung ya jaddada cewa babu wanda ya yaudari mutanen Pilato wajen kare ƙasar su, domin rikicin ya samo asali ne daga juyin mulkin 15 ga Janairun shekarar 1966.
Juyin mulkin da yayi sanadiyyar kisan shugabannin Arewa, ciki har da ɗan asalin Pilato, Kanal James Pam.
“Kisan da aka yi wa Kanal James Pam kaɗai ya isa ya tunzura mutanen Pilato wajen kare ƙasar nan” Inji shi.
Dalung ya nanata cewa tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Yakubu Gowon shi ne ya jagoranci Najeriya a lokacin yaƙin, ɗan jihar Plateau ne dake raye.
“Idan har da akwai buƙatar ban-haƙuri, Gowon ne ya dace ya yi, ba wanda yake yaro ƙarami a lokacin yaƙin ba.” Inji shi.
Ya ƙara da tambayar Gwamnan Muftwang ko akwai wani sashe na tsarin mulki ko al’ada da ya bashi ikon gabatar da ban-haƙurin a madadin al’umma, ba tare da tuntuɓar Sarakuna, magabata, ko Wakilai ba?
Daga ƙarshe, Dalung ya yi kiran cewa maimakon haifar da saɓani a lokacin da jihar ke fama da ƙalubalen tsaro, ya kamata shugaban ya maida hankali wajen haɗa kan jama’a da kuma kawo ƙarshen zubar da jinin dake damun jihar a yanzu.
