Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu, ya ba da umarnin gudanar da wani samame na tsawon kwanaki 14 a faɗin Jihar Benue domin kamo masu rike da makamai ba bisa ka’ida ba da kuma lalata maboyar masu aikata laifuka. Matakin na daga cikin sabbin ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar rashin tsaro a jihar.

Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Jihar Benue da ke Makurdi ranar Juma’a, Disu ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su tabbatar da kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a jihar.

Ya kuma jaddada cewa jami’an tsaro da aka ba izini ne kaɗai suka halasta su riƙe bindigogi, yana mai gargaɗin cewa duk wanda aka samu da makami ba bisa ka’ida ba zai fuskanci hukunci.

IGP ɗin ya ce an umarci jami’an ‘yan sanda su ƙara tsaurara matakan yaƙi da makamai ba bisa ƙa’ida ba, tare da ɗaukar matakin gaggawa bisa tanadin dokar 237 idan suka gamu da masu aikata laifuka ɗauke da makamai.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro har sai an dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.

A nasa jawabin, Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai kula da Rundunar Mopol, Francis Iduh, ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun gano manyan wurare 14 da ake yawan fuskantar hare-hare, waɗanda za su kasance cibiyar wannan aiki na musamman.

Ya ce yankunan da aka ware sun haɗa da Gbajimgba da Arufu da Agasha da Kwande da Agatu da Naka da Otukpo da Makurdi sai Apa da sauran al’ummomin da ke cikin haɗari. Ya ƙara da cewa za a ƙarfafa sintiri a dazuka da gonaki da sauran wuraren da ake zargin masu laifi na buya.

Iduh ya ce aikin na kwanaki 14 zai mayar da hankali ne wajen fatattakar makiyaya masu ɗauke da makamai, da ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka ba tare da muzgunawa mazauna yankunan da ke bin doka ba.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin sauƙaƙa kama masu laifi, yana mai tabbatar da cewa aikin zai kasance bisa bayanan sirri tare da haɗin gwiwar al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *