Dakarun Operation Hadin Kai tare da haɗin gwiwar kungiyar mafarauta ta Jihar Yobe sun cafke mutane biyar da ake zargi da garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Fune ta Jihar Yobe.

Rundunar ta ce aikin, wanda aka gudanar ranar 23 ga Yuli, 2026 a ƙauyen Jegalari, ya biyo bayan sahihin bayanan sirri kan ayyukan waɗanda ake zargin.

A yayin samamen, sojojin Bataliya ta 233 da ke Damaturu sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 da aka ƙera a gida guda uku da bindiga kirar hannu guda ɗaya da harsasai da kuma wayoyin hannu guda huɗu da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan laifi.

Waɗanda ake zargin suna hannun sojoji tare da kayayyakin da aka kwato domin ci gaba da bincike kan zargin hannu da suke da shi a ayyukan garkuwa da mutane da sauran laifuka.

Operation Haɗin Kai ta ce za ta ci gaba da gudanar da ayyukan leƙen asiri domin dakile masu aikata laifuka a yankin Arewa maso Gabas, tare da kira ga jama’a su riƙa bayar da bayanan da za su taimaka wajen ƙarfafa tsaro.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *