Jamus ta naɗa Jurgen Klopp a matsayin sabon kocin tawagar ‘yan wasan ƙasar, domin maye gurbin Julian Nagelsmann.
Sai dai Klopp ya yi gargaɗin cewa zai yi murabus daga sabon aikinsa na kocin Jamus idan kafafen yaɗa labarai na Jamus ba su “bar iyalinsa cikin lumana ba”.
Klopp ya dawo fagen horarwa da kwantiragi da zai ƙare a ƙarshen Gasar cin Kofin Duniya ta 2030. Ya bar Liverpool a 2024 bayan lashe kofuna 6 a cikin shekaru 9 da ya yi a ƙungiyar.
-
Gasar cin Kofin Duniyar da ba Najeriya a ciki, ba cikakke ba ne – Shugaban CAF Motsepe
-
Arsenal ta sayi Tzolis daga Club Brugge kan fam miliyan 34
-
Super Falcons za ta samu dala miliyan 2 idan ta…
An gabatar da ɗan shekaru 59 a ranar Juma’a, yayin da ya gargaɗi ‘yan jarida kan yadda suka soki magabacinsa Julian Nagelsmann.
“Manufata ita ce in inganta tawagar, kuma muna da ‘yan wasanni da yawa,” in ji Kloop.

“Za a biya ni kuɗi mai yawa. Kuma idan gobe suka ce Jurgen Klopp ba shi da amfani, zan tafi.
“Kuma idan ku ka nuna mummunan hali, ba ku bar iyalina sun zauna cikin lumana ba, zan tafi. Zan juya na tafi. Na san akwai ƙasashe da ake yi wa kocin tawagar ƙasar abu mafi muni fiye da haka. Ina son wannan aiki amma kuma ina shirye in bar shi.”
Klopp ne mutum na farko da DFB ta tuntuba bayan Nagelsmann ya yi murabus, sakamakon ficewar da ta yi ba tare da burgewa ba a Gasar cin Kofin Duniya, inda Paraguay ta fitar da su a bugun fenareti a zagaye na 32.
Amma Klopp ya kuma yi gargaɗi cewa naɗinsa ba zai tabbatar da nasara ba, kuma ana buƙatar a rage dogon buri.
Wasansa na farko a matsayin kocin Jamus zai kasance da ƙasar Holland a gasar Nations League a ranar 24 ga Satumba.
