Wasu jiga-jigan jam’iyyar ADC sun jagoranci wani taron zanga-zanga zuwa ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), imda suka mika wata takardar korafe-korafe.
Masu zanga-zangar sun yi dafifi a hedkwatar INEC ta kasa domin nuna rashin amincewarsu da wasu matakai da suka ce Hukumar ta ɗauka kwanan nan.
- Ya kamata Tinubu ya farka daga barci –Atiku
- Jam’iyyar ADC ta yi watsi da jita-jitar saukar David Mark
A wasiƙar da iyayen jam iyyar suka miƙa wa INEC, sun buƙaci shugaban Hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya sauka daga jagorancinta, bisa zargin katsalandan a cikin rikicin shugabancin jam iyyar.
Haka kuma jam’iyyar ta buƙaci INEC ta gaggauta mayar da sunan Sanata David Mark cikin kundin bayanan Hukumar a matsayin halaltaccen shugaba.

ADC ta zargi shugabancin INEC da ƙoƙarin mayar da ƙasar nan mai bin tsarin jam’iyya guda, ta hanyar raunana manyan jam’iyyun hamayya.
A ƙarshe jam iyyar ADCn ta buƙaci INEC ta mutunta hukuncin kotun da ya tabbatar da sahihancin shugabancin Sanata David Mark, da kuma takarar mambobinsu a zaɓukan da suka gabata.
A makon jiya ne dai Hukumar ta INEC ta sanar da cewa ta cire sunan Sanata David Mark da na Ogbeni Rauf Aregbesola daga kundin adana bayananta a matsayin Shugaba da Sakataren ADC na kasa daki-daki.
Hukumar ta ce ta dauki wannan mataki ne don bin umarnin wata kotu, wadda ta yanke hukunci a kan cewa a koma gidan jiya a batun shugabancin jam’iyyar.