Shugaban Kwamitin Tsaro da Al’amuran Ketare na Majalisar Dokokin Iran, Ebrahim Azizi, ya gabatar da wani sabon kuduri da zai haramta wa Amurka da Isra’ila wucewa ta Mashigar Hormuz.

Azizi ya yi wannan bayanin ne a gidan rediyo da talabijin na kasar Iran (IRIB), inda ya ce da zarar ƙudirin ya zama doka, Iran za ta haɗa gwiwa da kasar Oman don ƙarfafa ikon da take da shi a mashigin ruwan.

Ɗan majalisar ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na shirin da Iran take yi don ganin cewa yanayin tsaro a Mashigin Hormuz bai koma yadda yake kafin ɓarkewar rikicin da ya faru a watan Fabarairun da ya gabata ba.

Ƙudurin da a yanzu ya fara ɗaukar hankali, idan ya tabbata doka zai haramta wa Amurka da Isra’ila da dukkanin ƙawayensu wucewa da kayansu ta wannan yanki har abada.

Sannan ƙudirin dokar bai tsaya ga jiragen dakon mai ba, hatta jiragen ruwa da suke jigilar kayan amfani zuwa Isra’ila ko kuma yake fitowa daga can ya shafa.

Azizi ya jaddada cewa wannan haramci zai shafi kowace ƙasa da take ɗaukar matakai na adawa da ƙungiyoyin da Iran take mara wa baya a yankin Gabas ta Tsakiya, wato Resistance Front a Turance.

Matakin na zuwa ne a matsayin martani a takun saƙar da ake yi a yankin, inda Iran take ƙoƙarin yin amfani da ƙarfin da take da shi a mashigin ruwan na Hormuz don matsa lamba ga maƙiyan ta da kawayen su.

Mashigin Hormuz yana cikin mafi muhimmanci a duniya, domin kusan kashi daya bisa biyar na man fetur ɗin da duniya take amfani da shi yana bi ne ta wannan mashigi.

Idan har Iran ta aiwatar da wannan doka, hakan ka iya haddasa tashin farashin man fetur a duniya da kuma ƙara rura wutar rikici tsakanin ta da kasashen Yamma.

Kawo yanzu, ana kallon wannan a matsayin wata babbar barazana ga harkokin kasuwancin teku na duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *