An saken buɗe masallacin ƙudus, bayan ya shafe kwanaki 40 a rufe.

Wannan labari mai daɗi da ya riski al’ummar musulmin duniya ranar Alhamis, inda mahukuntan Isra’ila suka sake buɗe masallacin kwanaki 40 cur da hana shigar sa sakamakon dokar ta-ɓaci da aka sanya.

Tun da asubahin fari a ranar ta Alhamis kiran Sallar farko ya zame wa al’ummar dake maƙotaka da masallacin wani al’amari da suke fatan gani a rayuwarsu.

Ƙofofin masallacin da ke can cikin tsohon birnin ƙudus sun kasance a buɗe, yayin da ɗaruruwan Falasdinawa ke kwarara zuwa harabar sa

An gudanar sallar Asubahi cikin jam’i, a masallacin a karon farko, al’amarin da ya zanto na bazata ga dukkanin waɗanda labarin ke zuwa kunnuwan su a wannan rana.

Ko da yake, ba wai iya masallacin ƙudus wannan dokar ta ɓaci ta shafa ba har da ɓangaren bautar kiristoci da ake kira da Cocin Holy Sepulchre.

Hukumomin Isra’ila na sa ran buɗe cocin ne ga masu ziyara da masu ibada tun daga safiyar yau Alhamis.

Tun a ranar 28 ga watan Fabarairun wannan shekara ne Isra’ila ta bayyana rufe wuraren ibadun, biyo bayan yaƙin da take yi da Iran. lamarin da ya jefa yankin gabas ta tsakiya cikin halin rashin tabbas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *