Inspeta Janar Olatunji Disu.

Babban Sufeton ‘Yan Sanda na Najeriya Olatunji Disu ya gana da tsofaffin ‘yan sanda da suka fara zanga-zanga a Hedkwatar ‘Yan Sanda dake Abuja kan rashin biyan su haƙƙoƙinsu.

Da safiyar ranar Litinin ne tsofaffin jami’an suka hallara a gaban Hedkwatar inda suka bayyana muradunsu gare shi.

Sufeton ‘yan sandan ya saurari dukkan matsalolinsu da suka hada da bukatar fitar da su daga tsarin fansho na bai daya, tare da mayar da su tsohon tsarin da sojoji da jami’an DSS ke kai a yanzu

Tsaffin ‘yan sandan sun koka cewa kudaden da suke karba a ƙarƙashin sabon tsarin fansho ba ya iya ciyar da su ko biya musu bukatun magani, kamar yadda tsohon tsarin da suke kai ke zame musu adashen gata.

Har ila yau masu zanga-zangar sun bukaci a dubi garatuti da alawus-alawus dinsu da suka makale, suna gabatar da koke a kan cewa da yawa daga cikinsu sun dade da ritaya amma har yanzu ba su sami kudaden sallama ba.

Da yake ba su tabbaci, Babban Sufetan yan sanda Olatunji Disu, ya tabbatar musu cewa zai mika koken su ga shugaban kasa, tare da bibiya har sai an samar musu mafita.

A shekaru biyun da suka gabata tsofaffin ‘yan sanda sun gudanar da makamanciyar zangar zangar anan Abuja da wasu manyan jihohin kasarnan domin neman a fitar da su daga tsarin fanshon na bai daya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *