Shin da gaske kamfanonin jiragen sama za su dakatar da aiki kamar yadda rahotanni ke yawo a dandalin sada zumunta?
Akwai fargaba da rade-radin cewa kamfanonin jiragen sama na gida a Najeriya na shirin dakatar da zirga-zirga sakamakon ci gaba da tashin farashin man jirgi.
Wannan batu dai ya fito fili ne bayan wasu rahotanni daga kafafen yada labarai na kasashen waje da dandalin sada zumunta ke nuna yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin man fetur ke barazana ga bangaren sufuri, har da na jiragen sama.
Duk da wadannan rahotanni, bincikenmu ya nuna cewa har ya zuwa yau Alhamis, ana ci gaba da tashi da sauka a manyan filayen jirgin kasar kamar na Abuja da Legas.
Sai dai akwai manyan kalubale guda biyu da fasinjoji ke fuskanta da suka hadar da rashin tashin jiragen akan lokaci, da kuma tashin gwauron zabi da kudin tikiti keyi.
To amma masu ruwa da tsaki na ganin karin kudin shine yafi sauki, maimakon ace kamfanonin sun daina aiki. Suna ganin hakan zai sanya a samun biyan bukata a bangaren kamfanoni da fasinjoji.
Rahotanni na nuni da cewa farashin man jirgin ya tashi ne sannu a hankali daga naira 900 kan kowacce lita, zuwa kusan naira 3000. Karin da ake dorawa akan yakin dake faruwa a yankin gabas ta tsakiya, duk da cewa matatar Dangote na tace man a cikin gida.
Koda yake kungiyar masu kamfanonin jiragen sama AON ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance da ke cewa an dakatar da aiki ba a yau, amma tana ci gaba da yin kira ga gwamnatin tarayya da ta shiga cikin lamarin don samar da dauki kan farashin mai da kuma saukin samun dalar Amurka don siyo kayan gyaran jirgin daga waje.
