Gwamnatin Iran ta yi barazanar janye amincewarta daga tattaunawar da za a yi ta tsagaita wuta a tsakaninta da Amurka.

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim na ƙasar Iran ne ya ruwaito gwamnatin tana yin wannan barazana, tana mai cewa idan har Isra’ila ba ta daina kai hare-hare a kasar Lebanon ba za ta janye daga tattaunawar.

Iran ta bayyana cewa ci gaba da kai hare-hare a kan Lebanon ya saɓa wa yarjejeniyar da aka cimma, wanda hakan ke barazana ga zaman lafiyar yankin.

Wannan mataki na nuna cewa Iran a shirye take ta mayar da martani idan har sojojin Isra’ila ba su daina kai hari kan Lebanon ba.

Ana tsoron janyewar Iran ka iya jawo ƙaruwar farashin mai a duniya da kuma faɗaɗa yaƙin zuwa sauran sassan duniya.

Bayan da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya bayar da sanarwar dakatar da kai mata hare-hare na tsawon mako biyu ne dai Iran ta bayar da wasu sharudda da suka hada da dakatar da kai wa Hezbollah hari.

Sai dai Isra’ila ta ce tsagaita wutar ba ta shafi Lebanon ba, ta kumma kaddamar da hare-hare da dama a lokaci guda, wadana suka sanadin mutuwa mutum sama da 50 a kasar ta Lebanon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *