Iran ta ce ta yarda ta hau teburin shawarwari da Amurka, inda ta gabatar da sharuddan 10 da take so a tattauna a kai.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce ya karbi wadannan bukatu kuma za su iya kasancewa dan-ba a tattaunawar da za a yi.

Ga bukatun na Iran guda 10:

  1. Gamsasshen tabbaci daga Amurka cewa ba za ta sake kai wa Iran hari ba.
  2. Bai wa Iran iko da Mshigin Hormuz mai muhimmanci ga tattalin arzikin duniya.
  3. Amincewa da hakkin Iran na ci gaba da sarrafa makamshin nukiliya.
  4. Dage manyan takunkumin da aka kakaba wa tattalin arzikin Iran.
  5. Janye dakarun Amurka daga Gabas ta Tsakiya.
  6. Biyan Iran diyyar baranar da aka yi mata a yakin.
  7. Kawo karshen matakan soji a kan Iran da kawayenta, ciki har da wadanda suke Lebanon.
  8. Dage takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa Iran.
  9. Dage takunkuman da Hukumar Kula da Makamshin Nukiliya ta Duniya ta kakaba wa Iran.
  10. Tabbaci daga kasashen duniya cewa za a aiwatar da wadannan sharuddan.

Sai dai manazarta suna ta diga ayar tambaya a kan ko yiwuwar wadannan sharudda sus amu karbuwa idan aka hau teburin shawarwari.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *