Donald TrumpShugaba Donald Trump na Amurka ya ce bukatun da Iran ta gabatar guda 10 abin dubawa ne (Hoto: AP)

Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya sanar da jingine shirinsa na yin ruwan bama-bamai a kan Iran har tsawon makwanni biyu.

Da yake bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a kafar Truth Social, Shugaba Trump ya ce ya yanke shawarar ne bisa buƙatar Fira Minista Shehbaz da Babban Hafsan Tsaro Asim Munir na Pakistan.

Trump ya ƙara da cewa ya jingine aniyar tasa ne bisa sharaɗin cewa Iran za ta buɗe Mashigar Hormuz nan take.

“Na amince na dakatar da ruwan bama-bamai da kai hare-hare a kan Iran na tsawon makwanni biyu.

“Wannan yarjejeniyar tsagaita wuta ce mai kaifi biyu!

“Dalili kuma shi ne mun riga mun cimma burinmu ta fuskar matakan soji mun kuma yi nisa wajen samun zaman lafiya mai ɗorewa da Iran”, inji Trump.

Za mu bude, amma…

Wata sanarwa da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya fitar ta ce Iran ta amince ta buɗe Mashigar Hormuz a makwanni biyu masu zuwa bisa sharaɗin za a dakatar da kai mata hare-hare.

“Idan aka dakatar da hare-hare a kan Iran, Zaratan Dakarun Sojinmu za su dakatar da matakan kare-kai da suke ɗauka.

“A cikin makwanni biyu, shigewa ta Hormuz zai iya yiwuwa da haɗin gwiwar Dakarun Iran bisa la’a kari da abin da ba a rasa ba”, inji sanarwar, wadda Araghchi ya ce ya fitar a madadin Majalisar Ƙoli ta Taron Iran.

Ya kuma ce baya ga amsa buƙatar Fira Minista Sharif, Iran ta amince da wannan matakin ne bisa sanarwa Trump cewa ya karɓi sharuɗɗa 10 da mahukunta a Tehran suka gabatar.

Hare-Haren Isra’ila

Sai dai yayin da Shugaba Trump ke dakatar da aniyarsa, Isra;ila ta ci gaba da kai hare-hare.

Jairdar The Times of Israel ta ambato Fira Minista Benjamin Netanyhau yana yin maraba da wannan mataki, yayin da ta ruwaito wani jami’i yana cewa duk da tsagaita bude wutar kasar ta Yahudu ta ci gaba da kai hari.

Ranar Talata ne dai Mista Trump ya yi barazanar kawar da Iran daga doron kasa yana mai cewa ba za ta sake farfadowa ba har abada.

Wasu manazarta dai suna ganin wannan buƙata ta dakatar da hare-hare da shugabannin Pakistan suka gabatar ta tsamo Shugaba Donald Trump daga wani yanayi na tsaka-mai-wuya da ya jefa kansa a ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *