Paparoma Leo na goma sha-hudu (XIV) ya ce sau da yawa kwadayin mulki da son duniya, wadanda suka yi hannun riga da tafarkin Yesu (Annabi Isa, alaihissalam), kan sa a jirkita karantarwar Addinin Kirista.
Paparoman ya fadi haka ne a lokacin da yake jagorantar ibadar Mass gabanin Ista a birnin Roma ranar Alhamis.
Ko da yake bai ambaci sunan kowa ba, Paparoma Leo XIV yana mayar da martini ne ga kiran da Sakataren Tsaro na Amurka, Pete Hegseth, ya yi ga Amurkawa da su yi ta addu’o’i don samun nasarar kasarsu a yakin da ta kaddamar sama da wata guda a kan Iran.
“Mukan dauki kanmu wasu masu izza idan muka yi galaba, masu nasara idan muka hallaka sa’o’inmu, madaukaka idan ana tsornmu”, inji Paproma, wanda ya kara da cewa, “Allah Ya ba mu misali, amma na na yadda za mu yi mamaya ba, sai dai na yadda za mu ’yantar; ba na yadda za mu hallaka rayuka ba, sai dai mu raya”.
A karshen watan Maris ma Paparoma Leo XIV, wanda shi ne paparoma na farko haifaffen Amurka, ya yi gargadi game da ambata sunan Annabi Isa don yaki, yana cewa, “Yesu bay a saurarar addu’ar masu kaddamar da yaki, hasali ma fatali yake yi da ita”.
Mista Hegseth dai ya bukaci Amurkawa ne su “durkusa a kan gwiwa a kullum” su yi addu’a Amurka ta yi nasara a yakin da take yi a Gabas ta Tsakiya “da sunan Yesu Almasihu”.
Tun bayan da Amurka da Isra’ila suka fara Ruwan bama-bamai a kan Iran a karshen watan Fabrairu ne Paparoman yake ta kira da a dakatar da fadan a koma teburin shawarwari.
