Hankulan wasu ’yan Najeriya sun tashi bayan da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fitar da sanarwa cewa za ta fara tace kundin rajistar masu zabe a wannan watan.
Kurar ta tashi ne dai bayan labarin bullar wata takarda a kafofin sadarwa na zamani da aka ce an kwarmato tana dauke da bayanin hakan.
’Yan kasa da dama dai sun fassara wannan mataki da cewa INEC tana bukata ne ta sauya katunan zabensu, suna fargabar cewa wadanda ba su je ofishin hukumar, ko kuma sun shiga shafinta na intanet an tantance su ba, za su yi asarar kuri’unsu.
Su kuwa wasu jam’iyyun siyasa ayar tambaya suka diga game da sanar da wannan aiki a daidai wannan lokaci.
A wata sanarwa da ya fitar, Sakataren Yada Labarai na Kasa na jam’iyyar ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya nuna damuwa game da lamarin, yana gargadin cewa matakin ka iya haddasa rudani.
“Gamsar da ’yan kasa su fita su yi rajista abu ne mai wahala; yanzu kuma a bukace su su sake fita don “sabunta” rajistarsu tamkar ce musu ne kada su damu kansu”, inji Malam Bolaji.
Jam’iyyar ta ADC ta kuma yi zargin cewa APC kadai za ta amfana da wannan mataki.
Me INEC Take Nufi
Sai dai a wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ranar Juma’a, INEC ta ce wannan aiki, wanda za ta fara daga ranar 13 ga watan Afrilu, ba na sake rajista ba ne.
A cewar Hukumar, za ta yi bitar kundin masu zabe ne da suka yi rajista a tsakanin shekarar 2011 da 2024 da nufin fitar da sunayen mutanen da suka yi fiye da sau daya, da wadanda suka riga mu gidan gaskiya.
INEC ta kara da cewa wannan aiki zai kuma bayar da dama ga wadanda abin ya shafa su gyara kusakuran da aka yi yayin yi musu rajista – kamar kuskure wajen rubuta suna da makamantansa.
Wasu kungiyoyin farar hula sun yi maraba da wannan mataki, suna masu cewa hakan zai sa a tsaftace kundin rajistar masu kada kuri’a.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Shugaban kungiyar YIAGA mai fafutukar hanin an dama da matasa a harkokin siyasa da shugabamci a Afirka, Mista Samson Itodo, ya tabbatar da bukatar yin wannan aiki.
“Aikin tantance masu zabe da INEC ta jima tana magana a kai hanya ce mai kyau ta ta tsaftace kundin rajista”, inji Mista Itodo.
Sai dai a kara da cewa, “akwai matsala a lokacin da aka ayyana don gudanar da aikin – a halin yanzu jama’a ba su san tsari da girma da matakai da tasirinsa ba.
“Tantance masu zabe aiki ne da yake da tasiri a siyasance da ma a kan sakamakon zabe, don haka lokacin da aka ayyana don aiwatar da shi yana da matukar muhimmanci”.
Me Ya Jawo Takaddama?
Ba wannan ne dai karo na fark oba da INEC ta tace rajistar masu zabe gabanin manyan zabubbuka a Najeriya.
Bambancin shi ne a wannan karon an bukaci wadanda suka yi rajista su fita kwansu da kwarkwata don su tantance sunayensu.
Sannan kuma a maimakon yadda a baya Hukumar take tace rajistar a ofisoshinta, wannan karon an bukaci ’yan kasa su tafi ofisoshinta don a tantance bayanansu – kama daga sunaye zuwa hoton ’yan yatsu.
Mai yiwuwa wannan ne ya da mutane da dama suke zargin cewa INEC ta soke daukacin rajistar masu zabe tana bukata su je su sake.
Masu wannan ra’ayi sun kuma yi zargin cewa wani yunkuri ne na hana magoya bayan ’yan adawa kada kuri’a ranar zabe.
Sai dai kuma Shugaban INEC Farfesa Joash Amupitan ya kare matakin yana cewa ya zama wajibi don a tabbatar da inganci da sahihancin zabubbuka na gaba.
Da yake jawabi ga shugabannin kungiyoyin farar hula da na kafofin yada labarai a watan Fabrairu, Farfesa Amupitan ya ce, “Sahihin kundin rajistar masu kada kuri’a ne kashin bayan ingantaccen zabe, sahihi kuma na gaskiya”.
A credible register remains the bedrock of free, fair and transparent elections. No electoral process can command public confidence without trust in the integrity of its voters’ register,” Prof. Amupitan said, adding that the revalidation exercise would further sanitize the register ahead of 2027.
Wayar Da Kai
Mai yiwuwa babban abin da ya jawo tayar da jijoyoyin wuya a kan wannan batu a daidai wannan lokaci shi ne karancin wayar da kan al’umma game da lamarin, kamar yadda Mista Itodo na kungiyar YIAGA ya fada.
Sannan kuma ga shakkun da wasu ’yan Najeriya, musamman ’yan adawa suke nunawa game da yiwuwar gdanar da wannan aiki ana kasa da shekara guda kafin manyan zabubbika.
Ko ma dai mene ne zai biyo baya, lokaci ne zai tabbatar.
