Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da tsarin biyan basussukan da suka dabaibaye harkar wutar lantarki a Najeriya na tsawon shekaru goma, domin tabbatar da samun haske mai dorewa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban, Mista Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce Gwamnatin Tarayya ta tantance jimillar bashin da ya kai Naira Tiriliyan 3.3 wanda ya taru tun daga shekarar 2015 zuwa 2025.
Wannan mataki na nufin kawo ƙarshen rigingimun kuɗi da suka hana ɓangaren wutar ci gaba.
Sanarwar ta ce an fara biyan kamfanonin samar da wutar lantarki guda 15, waɗanda tuni suka riga suka sanya hannu a kan yarjejeniyar karɓar Naira Tiriliyan 2.3 daga cikin kuɗin.
Manufar biyan basussukan ba ta wuce bai wa kamfanonin damar sayen iskar gas da gyaran injina domin samar da wutar da za ta isa ko’ina ba.
Babbar mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara a kan Makamashi, Olu Arowolo-Verheijen, ta ce wannan shiri ba biyan bashi kawai ba ne, mataki ne na ganin masana’antu sun samu wutar da za su yi aiki, matasa su samu ayyuka, kuma gidajen ‘yan Najeriya su daina zama cikin duhu.
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan adawa suke caccakar gwamnati kan rashin tabbas a ɓangaren wutar lantarki, inda Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa za a shiga mataki na biyu na wannan garambawul nan ba da jimawa ba.