Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana damuwarsa kan abin da ya kira “kisan kiyashi” da ake yi wa mabiya Addinin Kirista a wasu sassan duniya, musamman a Najeriya da kuma yankin Gabas ta Tsakiya.
A sakonsa na bikin Ista da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Netanyahu ya ce yayin da mabiya Addinin Kirista ke bikin tashin Almasihu, da dama daga cikinsu suna fuskantar barazana ga rayuwarsu.
Netanyahu ya yi ikirarin cewa ana fuskantar kisan gilla a kullum a kan Kiristoci a Najeriya da kuma wasu sassan Gabas ta Tsakiya.
Ya nuna ɓacin ransa kan yadda ya ce ana kai hare-hare kan majami’u da kuma tsananta wa mutane saboda abin da suka yi imani da shi.
“Muna tare da ‘yan uwanmu Kiristoci wadanda ake zalunta saboda imaninsu. A Najeriya da Gabas ta Tsakiya, ana kisan gilla a kullum, kuma duniya ta yi shiru,” inji Netanyahu.
Daga nan ya yi kira ga kasashen duniya da su daina kawar da kai, maimakon haka su hada kai wajen yaƙi da tsagera da masu tsattsauran ra’ayi da ke kaddamar da wadannan hare-hare.
Kawo wannan lokaci dai mahukunta a Najeriya ba su mayar da martani kan kalaman na Netanyahu ba.
Najeriya na fuskantar matsalar sari-ka-noƙe a baya-bayan nan, matsalar dake ƙara raba kawunan ƙabilu da mabiya addinai biyu mafi girma a ƙasar nan.