Hukumar Jin Daɗin Alhazzai ta Jihar Kaduna ta bayyana wani gagarumin shiri na garambawul domin kauce wa matsalolin da aka fuskanta a Hajjin bara a shekarar bana.
Hukumar ta ce tana shirya tabbatar da biyan kuɗi da kammala takardun fasfo a kan lokaci.
Ɗaruruwan maniyyata ne suka rasa damar tafiya sauke farali a bara, sakamakon rage adadin kujerun da aka bai wa Najeriya.
Hukumar ta ce sauye-sauye a manufofin ƙasar Saudiyya da kuma jinkiri a ɓangaren maniyyata sun haifar da tsaiko a bara.
Da yake ƙarin bayani, kakakin Hukumar, Ibrahim Datti, ya ce maniyyatan shekarar da abin ya shafa za su iya karɓar kuɗaɗensu a ƙananan hukimominsu, ko kuma su bar shi a asusun ajiya na Hukumar domin shirin bana.
Ibrahim Datti ya ƙara da cewa akwai sabon tsarin adashin gata, domin bai wa maniyyata damar tara kuɗi a cikin sauƙi.
“Wannan tsarin zai taimaka wa maniyyata, musamman manoma da makiyaya, wajen yin tanadi tun kafin lokacin girbi ya kure musu, domin kauce wa dambarwar biyan kudi a kurarren lokaci,” inji shi
A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, Datti ya ce wasu daga cikin maniyyata na zargin an maye gurbinsu da wasu.
Sai dai, a cewarsa, jan ƙafar da suka yi ne ya haifar da haka.