Donald TrumpShugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa daya daga cikin waki'o'i mafi muhimminci a tarihin duniya zai faru ranar Talata da dare

Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa da maraicen Talata ɗaukacin tsarin rayuwar Iran zai kawo ƙarshe kuma ba zai farfaɗo ba har abada.

Trump ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social.

“Ba na son faruwar hakan, amma akwai yiwuwar ya faru”, inji Trump.

Idan ba a manta ba, Shugaban na Amurka ya bai wa Iran wa’adin zuwa ranar Talata da karfe 1 na dare agogon Najeriya ta buɗe Mashigar Hormuz ko ya kai hari a kan tashoshinta na samar wutar lantarki.

Trump ya kuma ce yana fatan ba za a kai ga haka ba “tun da an samu cikakken sauyi a shugabancin Iran inda wasu mutane na daban da suka waye kuma masu sassaucin ra’ayi [suke rike da iko]”.

Martani

Tuni Amurka da Isra’ila suka fara kai hare-hare a kan gadoji da tashoshin jiragen kasa a fadin Iran – inda Isra’ila ta gargadi jama’a da su kaurace wa jiragen kasa.

Hukumomin Iran dai sun yi kira ga al’ummar kasar, musamman matasa, su kewaye tashoshin samar da wutar lantarki don hana Amurka da Isra’ila kai musu hari.

An Ambato’yan jam’iyyar Democrat a Majalisar Dokokin Amurka suna cewa wanda ya zare ne kadai zai furta wadannan kalamai.

Masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum dai sun ce kai hari a kan ababen amfani farar hula – cibiyoyin kiwon lafiya da makarantu da gadoji – manyan laifuffukan yaki ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *