Mutane masu dimbin yawa suna gangami a sassa daban-daban na Iran yayin da ake cika kwana 40 da kisan Shugaban Addini Ayatollah Ali Khamenei.
Kafofin yada labarai na Iran sun bayar da rahoton cewa miliyoyin mutane ne suka fita kan tituna a Tehran, babban birnin kasar, da sauran birane don nuna alhininsu da rasuwar shugaban.
- Iran ta yi barazanar janyewa daga yarjejeniyar tsagaita wuta
- Sharudda 10 da Iran ta gindaya don tsagaita bude wuta
- Donald Trump ya dakatar da kai hari kan Iran
Ranar 28 ga watan Fabrairu ne dai wasu hare-haren hadin gwiwa da Isra’ila da Amurka suka kaddamar suka yi sanadin rasuwar Ayatollah Kahameni da wasu shugabannin kasar Iran.
Manyan hafsoshin sojin da aka kashe a ranar sun hada da Manjo Janar Abdolrahim Mousavi da Rear Admiral Ali Shamkhani da Manjo Janar Mohammad Pakpour.
Karantarwar Khamenei
A karantarwar mabiya Akidar Shi’a kwana 40 bayan mutuwa (Arba’in) lokaci ne mai matukar muhimmanci.
Gidan talabijin na Press TV ya ruwaito cewa a birnin Tehran, gangamin ya fara ne da safiyar Alhamis daga Dandalin Jomhouri, inda masu makoki suka yi tattaki zuwa wurin da aka kashe Khamenei.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, Rundunar Kare Juyin Juya-Hali ta Iran (IRGC) ta ce mutuwar Khamenei ta yi tasiri kamar yadda rayuwarsa ta yi.
Ta kara da cewa fikirar Kahamenei da fatawowinsa da salon jagorancinsa a bangaren turjiya da fafutukar neman ’yanci da adalci da yaki da zalunci da addini za su ci gaba da kasancewa tubali ga tsarin shugabancin kasar.
