Shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan,

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta dakatar da shirinta na tantance masu zabe har sai bayan zabubbukan 2027.

Wata sanarwa da Hukumar ta fitar mai dauke da sa=hannun Kwamishinanta mai kula da Harkar Yada Labarai, Mohammed Kudu Haruna, ta ce an yanke shawarar dakatar da shirin ne yayin wani taro da ta gudanar ranar Juma’a.

“Bayan tattaunawa mai zurfi, Hukumar ta yanke shawarar dakatar da aikin har sai bayan Manyan Zabubbukan 2027”, inji sanarwar.

Kwamishinonin zabe na jihohi ne dai suka hakarci zaman tattaunawar, a cewar sanarwar, ko da yake ba ta yi bayani ba a kan ko su suka nemi a dauki matakin.

Idan ba a manta ba, INEC ta sanar da cewa daga ranar 13 ga wannan wat ana Afrilu za ta fara aikin tantance masu katin zabe da nufin tace kundin sunayen masu rajista.

Sanarwar ta kara da cewa aikin tantance masu zaben wani muhimmin bangare ne na alhakin Hukumar “da nufin samar da sahihi kuma kammalallen kundin masu rajistar zabe a kasa”.

Ta kuma ce manufar aikin ita ce yin bita da tabbatar da bayanan masu zabe da cire sunayen wadanda suka yi rajista fiye da sau daya da kuma wadanda suka yi rajista shekarunsu ba su kai ba.

Tun bayan da INEC ta sanar da aniyarta ta gudanar da wannan aiki wasu ‘’yan Najriyas uke Allah-wadai suna zargin cewa wani yunkuri ne nah ana mutane kada kuri’a don amfani masu mulki.

Sai dai Hukumar ta kare kanta tana mai cewa aikin na tace kundin masu rajista ne ta hanyar bai wa mutane dama su sabunta bayanai.

Da ma dai Hukumar kan tace kundin sunayen masu rafista gabanin manyan zabubbuka, said ai a wannan karon ne ta bukaci ’yan kasa su je ofisoshinta don a tantance su.

Wasu ’yan Najeriya dai, musamman kungiyoyin farar hula sun yi na’am da shi ko da yake sun nuna shakku game da yiwuwarsa a cikin lokacin da ake da shin a kasa da shekara guda kafin Babban Zaben 2027.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *