Sakataren Yada Labarai na ADC Bolaji Abdullahi ya ce ADC ba ta yarda da gaskiyar Joash Amupitan be

Takun sakar da ake yi tsakanin Hukumar Zabe ta Najeriya (INEC), musamman Shugabanta Joash Amupitan, da ADC ya dauki sabon salo, inda jam’iyyar ta adawa ta bukaci ya yi murabus nan take ko ta bijire.

Jam’iyyar ta yi wannan barazana ne a wata sanarwa da Sakataren Yada Labaranat na Kasa, Malam Bolaji Abdullahi ya fitar ranar Asabar.

Sanarwar dai ta biyo bayan zarge-zargen da aka yi cewa a baya ya wallafa wasu kalamai da suke nuna goyon baya ga jam’iyyar APC mai mulki.

“Bayanai na baya-bayan nan da suka alakanta wani sakon Twitter a 2023 da Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, Farfesa [Joash] Amupitan, ba abu ne mai daga hankali kadai ba, cin fuska ne ga mutuncin tsarin zububbukanmu”, inji Malam Bolaji.

Kakakin na ADC dai yana tsokaci ne a kan wata Makala da aka ruwaito cewa dan jarida kuma malamin jami’a dan Najeriya mazaunin Amurka, Farooq Kperogi ya wallafa, inda ya yi zargin cewa wasu sakwannin X da aka wallafa a wani shafi mai dauke da sunan Amupitan sun nuna goyon baya ga APC da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

‘Labaran Karya Ne…’

Da yake wallafa tsakure daga cikinsu, Farfesa Farooq ya yi zargin cewa sakwannin sun karya kwarin gwiwar da al’ummar Najeriyas uke da shi a kan kasancewar Amupitan dan-baruwanmu; sannan ya yi kira ga Shugaban na INEC ya yi murabus.

Tuni dai Babban Sakataren Yada Labari kuma Mashawarcin Shugaban INEC a Kan Jafofin Sadarwa, Adedayo Oketola, ya zargi masu unugulu-da-kan-zabo da wallafa sakwannin.

A wata sanarwa da ya fitar, Mista Oketola ya yi gargadin cewa masu shigar burtu da masu satar kamannin mutane a intanet suna amfani da sunayen mutane don yana labaran karya.

Ya kuma jaddada kudurin INEC a karkashin jagorancin Farfesa Amupitann a gudanar da sahihai kuma ingnatattun zabubbuka.

Sai dai ga alama wadannan kalamai ba su gamsar da ADC ba domin a cewar Malam Bolaji, a karkashin tsarin dimokuradiyya, wajibi ne mai kula da gudanar da zabe ya kubuta dafa duk wani zargi.

“Ba kawai dan ba-ruwanmu ya wajaba ya kasance ba, dole a shaida hakan ba tare da wani shakku ba.

“Wannan shi ne mafi karancin abin da ake zato daga duk wanda aka dora wa alhakin gudanar da sahihin zabe kuma na haskiya”, inji Malam Bolaji.

Ce-ce-ku-ce a Kan Amupitan

Ba wannan ba ce takaddama ta farko a kan Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan.

Ko a kwanan baya ma, kungiyoyin Musulmi a karkashin jagorancin Majalisar Koli ta Shar’iar Muslunci a Najeriya sun bukaci a sauke Amupitan, bayan da aka zarge shi da rubuta wata makala da ta nuna cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.

Kungoyiyin sun ce abin da Shugaban Hukumar ta INEC ya rubuta ya nuna karara cewa bas hi da amana don haka ba su da kwarin gwiwa cewa zai yi adalci a zabubbukan da zai shugabanci gudanarwa.

Majalisar ta Shari’a ta kuma yi barazanar cewa in har ba a sauke Amupitan ba, to al’unnar Musulmin Najeriya za ta kaurace wa Manyan Zabubbukan 2027.

Abin jira a gani dai shi ne: shin Farfesa Amupitan zai tsallake wadannan zarge-zarge ko kuwa nauyinsu zai danne shi ya tilasta mishi yar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda?

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *