Masu iya magana kan ce “hangen Dala ba shiga birni ba” – kafin kashin da ta kwasa a hannun Bournemouth a gida ranar Asabar, kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kama hanyar lashe Gasar Firimiya ta Ingila ta kakar bana.

Amma fa har yanzu tana da sauran fata – idan ta ta yi nasara a karshen makon nan a kan Manchester City ta kuma lashe sauran wasannin da suka rage mata.

Sai dai kuma wasu na iya ganin wannan da kamar wuya, domin kuwa a filin was ana Etihad za a kara, kuma Manchester City na fatan shan gaban kungiyar ta Arsenal ba don ta daga kofin kadai ba, ta kara da kafa tarihi a matsayin kulob din da ya fi yawan lashe wasanni a wata biyu na karshen kaka.

A yanzu, Arsenal ce take saman tebur da maki 70 yayin da Manchester City take da maki 61. Wato ke nan akwai bambancin maki tara a tsakaninsu.

Sai dai kuma yayin da Arsenal ta buga wasanni 32, City 30 ta buga – don haka idan yaran Pep Guardiola suka ci wasanni biyun sannan suka lallasa Arsenal a gida, to za su share tazarar da ke tsakaninsu.

Daga nan sai a fara wani sabon lissafin.

Wasa Farin Girki

Masana harkar kwallon kafa da sun yi hasashen cewa Arsenal tana da kashi 86 cikin 100 na damar lashe Gasar.

Amma fa sai sun yi nasara a wasannin da suka rage musu a kakar, watan wasansu da Newcastle (a gida) ranar 25 ga watan Afrilu, da wasansu da Fulham (a gida) ranar 2 ga Mayu, da wasansu da West Ham (a waje) ranar 10 ga Mayu, da karawarsu da Burnley (a gida) ranar 17 ga Mayu, sai kuma fafatawarsu ta karshe ta kakar da Crystal Palace (a waje) ranar 24 ga Mayu.

Kasancewar sun shafe kaka uku a jere suna kamala gasar a matsayi na biyu, matsin lamba ya karu a kan Mikel Arteta da yaransa su yakice lakabin da ake musu na “Kofi Haram”.

Da za su yi nasara a Etihad a karshen mako mai zuwa, to hankali zai kwanta a kan cewa sun daga Kofin Gasar Firimiya ta bana.

Kalubale a Manchester

Abin tambaya a nan shi ne: shin Manchester City za su kyale Arsenal ta biyo su har gida ta fi wasa?

Gazawar da ta yi bara wajen kafa tarihin lashe Gasar FIrimiya sau biyar a jere, za isa Manchester City ta fito da buri biyu: na farko, ta huce haushin rashin lashe gasar bara, inda Arsenal ta sha gabanta a matsayi na biyu; na biyu kuma ta tabbatar wa magoya bayanta da sauran masoya kwallon kafa cewa ita ce Giwar Gasar Firimiya.

Da hakan ne Pep Guardiola zai lashe Gasar Firimiya a karo na shida bayan ya kafa tarihin lashewa sau hudu a jere:

  • 2020/21
  • 2021/22
  • 2022/23
  • 2023/24

Maci Tuwo

A wasannin da Arsenal ta buga a kaka biyar da ta gabata, Manchester City ce ta fi yin galaba.

Amma a baya-bayan nan, tun bayan da Mikel Arteta ya karbi ragamarta, Arsenal ta yunkuro tana bayar da mamaki.

Ga yadda wasanninsu suka kasance a kaka biyar ta baya-bayan nan:

  • 2025/26      Arsenal 1–1 Man City      Kunnen Doki a Emirates
  • 2024/25      Arsenal 5–1 Man City      Nasarar Arsenal mafi girma a kan Pep
  •       ”              Man City 2–2 Arsenal      Canjaras a Etihad
  • 2023/24      Man City 0–0 Arsenal      Canjaras din da ya karya kwarin gwiwar City
  •         ”            Arsenal 1–0 Man City       Nasarar Arsenal bayan ta dade tana shan kashi
  • 2022/23      Man City 4–1 Arsenal        Nasarar da ta bude wa City kofar lashe Gasar
  •        ”               Arsenal 1–3 Man City        City ta nuna gwaninta
  • 2021/22       Man City 5–0 Arsenal       Farkon zuwan Arteta, Arsenal tana da rauni
  •         ”             Arsenal 1–2 Man City

Arsenal na fatan lashe Gasar Firmiya a karo na farko a shekara 20; shin Manchester City za ta bari ko kiwa?

Masu iya magana kan ce “Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *