Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta ce ta kaddamar da binciken kwakwaf a kan rahotannin kisan fararen hula da ke cin kasuwa a kan iyakar jihohin Yobe da Borno.
A wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Rundubar, Ehimen Ejodame, ya ce NAF ta dauki rahotannin da matukar muhimmanci.
“Rundunar Sojin Sama ta Najeriya tana duba rahotannin da suke zargin cewa akwai yiwuwar wani hari da aka kai ta sama ranar Asabar 11 ga Afrilun 2026 ya taba wata kasuwa a Jilli, lamarin da ya haddasa mutuwar farar hula”, inji sanarwar.
Rahotannin sun ce ranar Asabar wasu jiragen saman yaki na NAF uku suka kai hari a kan wata kasuwa da ke kauyen Jilli a Jihar Yobe kusa da iyakar Jihar Borno.
- Dakarun Operation Haɗin Kai sun daƙile hari a Benisheik
- Gwamnati za ta ɗauki mataki a kan kisan gillar Jos –Mutfwang
Ko da yake NAF ba ta bayyana adadin mutanen da abin ya shafa ba, an ba da rahoton cewa akalla mutum 100 ne suka rasa rayukansu a harin yayin da wasu da dama suka jikkata.
Da take Allah-wadai da harin, kungiyar Amnesty International mai fafutukar kare hakkin bil-Adama ta ce mutum sama da 100 ne suka mutu, tana ruwaito cewa zuwa lokacin da ta fitar da sanarwa a kan batun an kai mutum akalla 35 da suka yi munanan raubuka Babban Asibitin Geidam.
“Kaddamar da hari ta sama ba halaltacciyar hanya ba ce ta tabbatar da doka da oda a bisa ko wanne irin ma’auni.
“Irin wannan ganganci wajen amfani da karfin tsiya ya haramta, ya yi muni, kuma ya nuna yadda rundunonin sojin Najeriya suke rikon sakainar kashi wa rayuwar mutanen da aka samar da su don su kare”, inji Amnesty.
Kamfanin dillancin lanarai na AP ya ambato Daraktan Amnesty a Najeriya, Isa Sanusi, yana cewa a cikin wadanda aka kashe har da yara, “kuma muna da hotunansu”.
Maboyar Boko Haram
Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa (AFP) ya ambato Mai Unguwar yankin, Lawan Zanna Nur Geidam, yana cewa adadin mutanen da suka jikkata ko suka rasa rayukansu ya kai 200.
Tun da farko dai NAF ta sanar da cewa ta kai hari ne a kan wata maboya ta ’yan Boko Haram a yankin inda ta kashe wasu mayaka.
Sai dai daga bisani, a wata sanarwa mai dauke da sa-hannun mashawarcin Gwamna a kan al’amuran da suka shafi soji, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam, Gwamnatin Jihar Yobe ta ce an kai harin ne a kusa da wata kasuwa da ke cike makil da mutane.
Da yake tsokaci a kan lamarin, Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya ce shekaru biyar da suka wuce Gwamnati ta rufe kasuwar Jilli.
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dauda Iliya, ta fitar ta ambato Gwamnan yana cewa, “An yi min cikakken bayani game da harin da bangaren sojin sama na Rundunar Operation Hadin Kai ya kai a Kasuwar Jilli, wani gari da ke kan iyakar jihohin Borno da Yobe.
“Ina tabbatar da cewa ba tare da wani boye-boye ba, Gwamnatin Jihar Borno ta rufe kasuwannin Jilli da Gazabure shekaru biyar da suka gabata”.
Dalilin hakan kuwa, inji sanarwar, shi ne mayakan Boko Haram da masu kai musu kaya ne suke amfani da kasuwannin don saye da sayarwa.
Gwamna Zulum ya kuma bukaci jama’a da su guji bayar da mafaka ga ko boye ’yan ta’adda.
Ba wanann ne karo na fako ba da NAF ta kai hari bisa kuskure a kan farar hula.
