Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai a Najeriya Mohammed Idris ya jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta tallata hanyoyin tattalin arziki da al’adu da yawon buɗe ido na Najeriya a idon duniya.
Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da yake karɓar baƙuncin wata tawaga daga Hukumar da ke Sa Ido Kan Gidajen Jarida ta Najeriya (NPC) a ranar Talata.
Tawagar ta je ne domin yi wa Ministan bayanin yadda shirye-shirye suka yi nisa, na ƙaddamar da wani kundi da zai tattara hanyoyin samun arziki da ake da su a jihohin ƙasar nan 36, da Babban Birnin Tarayya.
Ministan ya ce wannan yunƙuri ya yi daidai da manufofin gwamnatin tarayya, a ƙoƙarin ta na fadada hanyoyin bunƙasar tattalin arziki ta hanyar yawon buɗe ido da al’adu da jawo masu zuba jari da kuma fadada hanyoyin samun kuɗaɗe ba tare da dogaro da man fetur kadai ba.
-
Rundunar sojin Najeriya ta karyata kisan mutum 100 a Zamfara
-
Yadda ‘kisan’ tsohon dan majalisa daga Jigawa ya firgita mutanen Abuja
“Wannan aiki yana da matuƙar muhimmanci domin zai haskaka dumbin hanyoyin samu ta fuskar tattalin arziki da yawon buɗe ido a ƙasar mu, a lokacin da wasu mutane suke mayar da hankali kan labaran ɓatanci game da Najeriya.
“Abin da kuke yi zai taimaka wajen nuna dumbin damarmakin da ke a fadin jihohi 36 da FCT,” in ji Ministan.
Mohammed Idris ya tabbatar wa tawagar cewa ma’aikatarsa za ta bai wa shirin cikakken goyon baya don ganin taron ƙaddamarwar ya yi nasarar da ake fata.
Sakataren hukumar ta NPC, Dokta Dili Ezughah, ya shaida wa Ministan cewa sun fito da wannan shiri ne domin haɗa ƙarfi da hukumomin gwamnati wajen tallata Najeriya a idon duniya.
Ya bayyana cewa littafin zai zama madogara ga masu zuba jari, ofisoshin jakadanci, da ‘yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen ƙetare, domin fadada hanyoyin samun kudaden shiga da kuma bunkasar tattalin arziki ga ƙasar.
An shirya gudanar da taron ne a ranar 17 ga watan Yunin shekarar 2026, a Fadar Shugaban ƙasa. Kundin ya ƙunshi cikakken bayani kan kowace jiha, da damammakin zuba jari, albarkatun ƙasa, yawan jama’a, ababen more rayuwa, da kuma rangwamen haraji ga ‘yan kasuwa.
