INEC zata yi amfani da masu bautar kasa sama da Miliyan guda a zabukan shekarar 2027

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya jagoranci wata tawagar hukumar zuwa helkwatar Hukumar Hidimar Ƙasa (NYSC) da ke Yakubu Gowon House a Abuja.

Yayin ziyarar, Farfesa Amupitan ya jaddada muhimmancin rawar da masu hidimar ƙasa suke takawa a tsarin dimokraɗiyyar Najeriya.

Ya ce INEC za ta nemi ma’aikatan wucin gadi sama da miliyan guda,  waɗanda akasarinsu za a ɗauko su ne daga cikin masu yi wa ƙasa hidima.

Farfesa Amupitan ya ce tun daga shekarar 1999 masu bautar ƙasa ne ginshikin samun nasarar ayyukan hukumar zaɓen INEC, a duk lokacin da suke rike da matsayin baturai na rumfunan zaɓe wato (Presiding Officers).

Shugaban na INEC  ya ce a wannan karon masu bautar ƙasa 707,384 ne zasu tafikar da aikin zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisun Tarayya a ranakun 16 ga Janairun 2027.

Haka kuma a zabukan Gwamnoni da na Yan Majalisun Jihohi a ranar 6 ga watan Fabrairun shekarar 2027.  Sai zaɓukan gwamnoni daga bisani a jihohin Ekiti da Osun, da kuma zaɓukan cike-giɓi a jihohin Nasarawa, Enugu, Rivers, Ondo, Kebbi, da Kano.

Game da batun tsaro kuwa, Amupitan ya ba wa shugabancin NYSC tabbacin cewa INEC ta himmatu wajen inganta tsarin inshora, jin daɗi, da kuma tsaron lafiyar duk wani mai bautar ƙasa da za’ a tura aikin zaɓe.

Da yake martani, Darakta Janar na NYSC Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ya ce dangantakar da ke tsakanin hukumomin biyu ta dade, inda yake bayyana masu bautar ƙasar a matsayin amintattu ‘yan kishin ƙasa, waɗanda ke da sauƙin horarwa.

“Sabon ƙarni na matasanmu na yanzu (Gen Z) sun kware sosai a fannin fasahar sadarwa (ICT), wanda hakan zai taimaka matuƙa wajen gudanar da zaɓukan zamani”, inji janar Olakunle Nafiu

Daga ƙarshe, Shugaban na NYSC ya yi kira ga INEC da ta ƙara inganta alawus-alawus da inshorar masu bautar ƙasar domin ƙarfafa musu gwiwar yin aiki tuƙuru ga ƙasarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *