Wasu mambobin Kungiyar Tuntuba ta Dattawan Arewa (ACF) sun kare Alhaji Bashir Dalhatu, sun kuma yi watsi da matakin dakatar da shi.
Sama da mambobi 70 na Kwamitin Amintattu (BoT) na ƙungiyar ne suka bayyana watsi da dakatarwar a garin Kaduna, a ranar Lahadi.
A wata sanarwa da dattawan ƙungiyar suka sanya wa hannu, wadda aka raba wa manema labarai, Mambobin sun bayyana cewa Kwamitin Zartarwar ƙungiyar (NEC) ba shi da ikon tsige shugaban kwamitin amintattun ta ko dakatar da shi.
Rukunin dattawan sun “la’anci matakin da suka kira da tsantsar rashin hankali da rashin hikima na wasu tsirarun mutane da suka kira masu neman tada zaune tsaye a cikin ƙungiyar, ya sanya su bayyana sanarwar dakatarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa matakin da tsirarun yan kungiyar suka ɗauka yaci karo tsarin mulkin (ACF), ƙa’idoji, dokoki. Hasalima basu da halaccin kiran kowane irin taro a madadin ta, wanda anan ne aka fitar da sanarwar dakatar da Alhaji bashir Dalhatu.
A ranar Larabar da ta gabata ne Majalisar Zartarwar Kungiyar (ACF) karkashin Shugabancin Mike Mamman Usuman ta dakatar da Shugaban Kwamitin Amintattu na kungiyar, Alhaji Bashir M. Dalhatu, bisa zargin rashin gaskiya wajen sarrafa kudade da kuma karya ka’idojin kundin tsarin mulkinta.
