Jam'iyyar APC ta kara wa'adi ga masu neman takara

​Jam’iyyar APC ta amince da ƙarin wa’adin sayen takardar tsayawa takara ƙarƙashin ta,  ga mabuƙata tsayawa takara a babban zaɓen shekarar 2027.

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran APC na kasa Felix Morka ya fitar, tace jam iyyar ta ware Laraba 6 ga watan Mayu domin dakatar da siyarwa.

Yayin da ranar Alhamis 7 ga watan Mayu zata kasance wa’adin ƙarshe na mayarwa, sai kuma Juma’a 8, zuwa Talata 12 ga watan Mayu a matsayin ranakun tantancewa.

Sanarwar ta bayyana Laraba 13 ga watan Mayu a matsayin ranar wallafa sunayen waɗanda suka tsallake tantancewa.

Gabanin fitar sanarwar, jam’iyyar APC a jihohin ƙasarnan ta dukufa wajen sasanta masu neman kujera guda, domin shiga zaɓe babu hamayya. Duk da cewa a jihar Gombe Farfesa Isa Ali Pantami na ganin zaben fidda gwani ne kaɗai mafita, domin kaucewa rikicin cikin gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *