An Kama Sale Mamman ne da sanyin safiyar ranar Talata a Kaduna

Hukumar EFCC ta kama tsohon Ministan Lantarki, Saleh Mamman, wanda aka yankewa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 75 saboda karkatar da kudi har naira biliyan 33.8 da aka ware don samar da tashoshin wutar lantarki a Zungeru da Mambilla.

Mamman, wanda ya kasance yana gudun hijira, an kama shi ne da sanyin safiyar yau da misalin karfe 3:30 na safe a Jihar Kaduna, tare da wasu mutane biyu da ke ba shi kariya. Haka kuma, a halin yanzu ana gudanar da bincike kan gidan da aka kama shi.

A ranar Alhamis 7 ga watan Mayun shekarar 2026 Mai shari’a Omotosho ya kama tsohon Ministan da laifi inda ya yanke masa hukuncin daurin shekaru 75 a gidan kaso a ranar Laraba, 13 ga watan Mayu, 2026, bayan da tsohon ministan ya ki bayyana a gaban kotu a ranar da aka kama shi da laifi.

Mai Shari’a Omotosho ya ce hukuncin zai fara aiki ne daga ranar da aka kama shi, 19 ga watan Mayun Shekarar 2026.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *