Babban Bankin Najeriya, CBN, ya canzawa dukkan mataimakan gwamnoni hudu matsayi a wani yunkuri na karfafa hadin kai tsakanin manyan sassan babban bankin.
Sauye-sauyen sun fara aiki ne a ranar 1 ga watan Yunin 2026, kamar yadda shafin Intanet na Babban bankin ya bayyana ranar Litinin.
Karkashin sabon tsarin, an mayar da Philip Ikeazor shugabancin Sashen Tsare-Tsare, inda ya karbi ragamar aiki daga Muhammad Abdullahi, wanda yanzu ke kula da Sashen Ayyukan Kamfanoni.
Kazalika, an dauke Emem Usoro daga Sashen Ayyukan Kamfanoni zuwa Sashen tsara ayyukan cikin gida, yayin da Lamido Yuguda, zuwa Sashen tabbatar da dai-daiton tattalin arziki.
Babban bankin ya ce canje-canjen na daga cikin yunkurin cin moriyar gogewar manyan shugabanninsa da kuma daidaita nauyin da ke kansu.
A cewar CBN, ana sa ran wannan sauyi zai inganta nagartar aiki da kuma karfafa hadin kai a tsakanin sassan bankin.
Sauye-Sauyen na baya-bayan nan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yin garambawul a babban bankin, yayin da yake kokarin karfafa tsarin manufofin kudi, tabbatar da dai-daito, da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa baki daya a cewar sanarwar.
Babban Bankin dai na fuskantar manyan kalubale da suka hadar da sarrafa makudan kudade da basussuka da suka aka gaza biya, tsadar kudaden rance ga kamfanoni da yan kasuwa sakamakon tsayuwar kudin ruwa akan kashi 26.5 domin yakar hauwar farashi.
