Kotu tace Jonathan za iya tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027

Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta sanya ranar Juma’a domin cigaba da sauraron karar da ke neman hana tsohon Shugaban Kasar Goodluck Ebele Jonathan sake tsayawa takara a zaben shekarar 2027.

Wani lauya mai suna Johnmary Jideobi ne ya shigar da karar yana bukatar kotun ta fassara masa ko a Tsarin Mulkin Najeriya Jonathan yana da ikon sake neman kujerar shugabancin Najeriya.

Lauyan ya kafa hujja da sassa na 1(1), (2), (3) da kuma sashe na 137(3) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 da aka yi masa kwaskwarima, wadanda suke cewa mutum ba zai iya rantsuwar kama aikin shugabancin kasa har sau uku ba.

Kamar yadda Emmanuel Agida, wanda ya shigar da karar, Jonathan ya riga ya rantse a ranar 6 ga Mayun 2010 bayan rasuwar Yar’Adua, sannan ya sake rantsuwa a 2011 bayan ya lashe zabe.

A ranar 28 ga watan Afrilu ne Mai Shari’a Peter Lifu ya bayar da umarnin isar da takardar sammaci ga wanda ake kara na farko, wato Goodluck Ebele Jonathan, da wadda ake kara ta biyu wato Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a matsayin wanda ake kara na uku, bayan da suka gaza mika bayanan kariyarsu a kan lokaci.

Babbar bukatar lauyan mai shigar da karar ita ce kotun ta hana Jonathan gabatar da kansa a matsayin dan takara ga kowace jam’iyyar siyasa, sai kuma hana INEC karba ko tantancewa ko kuma wallafa sunan Jonathan a matsayin dan takarar Shugaban Kasa a zaben 2027.

Karar na zuwa ne a daidai lokacin da rade-radin dawowar tsohon Shugaban Kasar harkokin siyasa ke kara karfi.

A ranar Laraba ne wasu matasa suka yi dafifi a gidan Jonathan dake Gundumar Maitama a Abuja, inda suka roke shi da ya fito takara a zabe mai zuwa domin “ceto kasar.”

A nan ne ya bayyana musu jin dadin sa game da wannan hange nasu, amma ya bayyana musu cewa ba zai yanke hukunci cikin sauri ba.

Jonathan ya jaddada cewa batun takara babban al’amari ne da ke bukatar zurfafa tunani da neman shawara, don haka yana kan gudanar da tuntuba da masu ruwa da tsaki a sassa daban-daban kafin ya ayyana matsayarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *