An samu takaddama mai zafi a zauren Majalisar Dattawan Najeriya a ranar Laraba, tsakanin Shugaban Majalisar Godswill Akpabio, da Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa Adams Oshiomhole.

Takaddamar ta barke ne kasa da kwana guda, bayan da Majalisar ta yi wa dokokinta kwaskwarima, inda ta sanya wasu ka’idoji masu tsauri ga masu burin zama shugabanninta nan gaba.

Musabbabin Rikicin.
Rikicin ya samo asali ne lokacin da Akpabio ya fara karanta bayanan zaman da Majalisar ta yi domin neman amincewar mambobi.

Nan take Sanata Oshiomhole ya tashi tsaye yana neman a ba shi damar nuna rashin jin dadin yadda aka tsara bayanan taron na ranar Talata.

Oshiomhole ya dage cewa takardar da aka gabatar ba ta yi daidai da abin da ya faru a zauren ba, game da batun kwaskwarimar dokar shugabanci da aka yi.

Sai dai Akpabio ya ki ba shi dama, yana mai cewa bisa ka’idar majalisa, ba a amincewa da ko wane irin tsokaci a daidai wannan lokacin har sai an gama amincewa da rahoton zaman da ya gabata.

Yayin da Oshiomhole ya ci gaba da magana ba tare da an ba shi izini ba, Akpabio ya fusata, inda ya ja kunnen Sanatan da cewa dole ya bi doka da tsarin Majalisar ko kuma ya kore shi.

“Sanata Oshiomhole, idan ka ci gaba da bijire wa dokokin Majalisa, zan ba da umarnin jami’an tsaro su fitar da kai daga zauren nan. Wannan ne gargadi na karshe”, inji Apkabio

A wannan gaba ne Babban Mai Tsawatarwa na Majalisar Sanata Tahir Monguno, ya sanya baki ta hanyar kokarin tsawatar wa Oshiomhole, inda ya bukace shi da ya bi doka ya zauna, amma dan majalisar ya ci gaba da daga murya har sai da aka kashe masa na’urar magana.

Me Sabuwar Dokar Ta Kunsa?
Wannan takaddama dai na da alaka da kwaskwarimar da majalisar ta yi wa dokar majalisar ta 2, 4 da 5″ a ranar Talata, 5 ga Mayu, 2026.

Sabuwar dokar ta tanadi cewa wajibi ne mai neman takarar Shugaban Majalisa ko Mataimaki ya kasance ya yi wakilci na wa’adi biyu a jere, wato ya kasance a kan wa’adi na biyu na tsawon shekaru (8) a jere a Majalisar Dattawa.

Sannan dole ne a bai wa tsofaffin shugabannin majalisa ko manyan kusoshi fifiko wajen takara, sakamakon gogewa da suke da ita a harkokin majalisar.

Wadannan dokoki gaba dayan su sun shafi Sanata Oshiomhole kai-tsaye, domin shi sabon Sanata ne da ya fara wakilci kasa da shekaru 4, hakan kuma yana nufin ba zai iya takarar shugabancin majalisa ba a shekarar 2027 idan har dokar ta ci gaba da aiki.

Bayan kusan mintuna 15 ana wannan dambarwa, an samu daidaito a karshe, inda har aka amince da rahoton zaman da ya gabata, daga nan kuma aka ci gaba da sauran ayyukan majalisa na wannan rana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *