Rikicin shugabancin da ya dabaibaye Kungiyar Tuntuba ta Dattawan Arewa (ACF) na ci gaba da murtukewa, lamarin da ka iya barzana ga tasirin yankin a siyasance.
Rikicin ya dauki sabon salo ne ranar Talata, bayan da ’yan sanda suka garkame babban ofishin kungiyar da ke Kaduna, lamarin da ya hana taron Majalisar Zartarwa ta Kasa (NEC) da aka shirya gudanarwa.
Jami’an tsaron sun kafa shingaye a sakatariyar, wadda ke kan titin Sakkwato Road, lamarin da ya kara fito da rarrabuwar kawuna a fili a tsakanin mambobin kungiyar.
Yayin da wasu kusoshin kungiyar ke nuna bacin ransu, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna ta ce tura jami’an ya zama dole domin kauce wa barkewar tashin-tashina a tsakanin bangarorin da ke jayayya da juna.
Majalisar Dattawa ta nemi a soke lasisin kamfanoni mallakar Afirka ta Kudu
-
Majalisar Dattawa ta nemi a soke lasisin kamfanoni mallakar Afirka ta Kudu
-
Minista ya roki masu kamfanonin jiragen sama da kada su daina aiki
Rundunar, ta bakin kakakinta DSP Mansur Hassan, ta ce ta samu wasikun bangarorin biyu dake bayyana shirinsu na gudanar da tarurruka daban-daban, lamarin da ya sanya ta gudanar da bincike tare da samun bayanan sirri cewa suna neman izinin gudanar da taron ne a lokaci guda.
Wannan ne, a cewarsa, ya sanya rundunar garkame ofishin domin kauce wa abin da ka iya biyo baya.
Mambobin Majalisar Zartarwar Kungiyar a karkashin jagorancin Barista Mamman Mike Osuman sun yi niyyar gudanar da taron gaggawa ne a sakataiyar kafin su iske lamarin ya sauya.
Dalilin rikicin
A wata sanarwa da ya fitar mai taken “Babban Ofishin ACF a garkame,” Mamman Mike Osuman ya soki Shugaban Kwamitin Amintattu , Alhaji Bashir Dalhatu, wanda ya zarga da yin katsalandan da wuce ka’idojin kundin tsarin mulkin kungiyar.
Osuman ya bayyana garkame ofishin a matsayin “Tozarci,” bayan da shi da sauran mambobin Kwamitin Gudanarwa suka tsinci kansu a kulle a ciki.
A bangare guda, Alhaji Bashir Dalhatu ya fitar da sanarwar raddi inda ya bukaci mambobin kugiyar da su kaurace wa taron, yana mai cewa haramtacce ne.
Ya ce Sakatare Janar na kungiyar, Malam Murtala Aliyu, ba shi da ikon kiran taro domin wa’adin mulkinsa ya kare tun ranar 10 ga watan Maris, 2026.
Baya ga batun shugabanci, akwai zarge-zargen rashin gaskiya wajen sarrafa fiye da Naira biliyan uku da aka tara wa kungiyar a taron neman tallafi da aka yi a shekarar da ta gabata.
Tuni ma dai Kwamitin Da’a na Kungiyar yana nazari a kan wani koke da aka shigar game da yadda aka tafiyar da kudin.
Shiga tsakani
Kafar yada labarai ta Nigerian Invoice ta ruwaito cewa akwai alamun Mai Alfarma Sarkin Musumi Alhaji Muhammadu Sa’adu Abubakar yana kokarin shiga tsakani, ko da yake Sakataren Majalisar Masarautar Sarkin, Alhaji Sa’idu Maccido, ya ce ba shi da masaniya kan wani yunkuri na sulhu da Sultan din ke yi a halin yanzu.
Wasu majiyoyi a kungiyar sun nuna takaicinsu kan yadda sabani ya shiga tsakanin shugabannin, wadanda ya kamata su hada kan Arewa gabanin zabuka masu zuwa.
Wani Mai sharhi kan al’amjuran tsaro, Mustafa Bature Sallama, ya gabatar da wata mukala dake nuna yadda yankin Arewa ke cikin matsananciyar matsalar rashin makoma da rashin tsaro ya haifar mata.
Ya ce barazanar ba ga asarar rayuka da ake yi yau da kullum kadai ta tsaya ba, tana shafar makomar Najeriya ne a matsayin kasa mai yanci.
Yana ganin akwai bukatar magabatan Arewa su kawar da bukatar kai domin sanya makomar al’umma gaba.
A halin yanzu, mambobin kungiyar da dama na kira ga iyayen kungiyar, ciki har da tsofaffin shugabannin kasa da su shiga lamarin domin ceto martabar kungiyar ta (ACF) kafin abubuwa su sake tabarbare mata.
