Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce idan Iran ta amince aka cimma yarjejniya da ita to yakin da ya kaddamar a kanta da hadin gwiwar Fira Minista Benjamin Netanyahu na Isra’ila, wanda aka yiwa lakabi da “Operation Epic Fury” zai kawo karshe.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya kuma yi barazanar idan kasar ta Iran ba ta amince ba za a ci gaba da yi mata uwan bama-bamai a matakin da ya fi yadda wanda aka yi mata a baya.
“Mu dauka cewa Iran za ta yarda da abin da aka amince…Epic Fury zai kawo karshe, kuma… za a bude Mashigar Hormuz ga kowa, har da Iran.
“Idan ba ta yarda ba, za a fara ruwan bama-bamai kuma, abin bakin ciki, wanda ya fi na da a mataki da tsanani”, inji Trump.
- Yadda ficewar UAE daga OPEC ka iya girgiza harkar danyen mai
- Iran ta gindaya wa Amurka sharadi game da nukiliya.
- Amurka ta toshe tashoshin jiragen ruwan Iran
Wannan barazana dai tana zuwa ne a daidai lokacin da wasu kafofin yada labarai suke bayar da rahotn cewa akwai yiwuwar cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran.
Shafi daya na sharadi
Kasar ta Amurka dai ta aike da wasu shawarwari ga Iran wadanda ta ce cimma yarjejeniya a kansu zai kawo karshen yakin sannan ya samar da wata manhaja ta tattaunawa a kan shirin makamashin nukiliya na Iran.
Shawarwarin sun hada da bukatar Iran ta amince da dakatar da sarrafa makamshin nukiliya har tsawon shekara 12, Amurka ta dage duk wani takunkumi da ta kakaba mata, ta kuma ba ta damar taba biliyoyin dalolinta, sannan bangarorin biyu su bude Mashigar Hormuz.
Tun da farko dai Trump ya dakatar da wani aiki da ya daukar wa kansa mai lakabin Project Freedom na bude wa jiragen ruwa hanya ta Mashigar Hormuz.
Da dama daga cikin shawarwarin na Amurka dai za su yi aiki ne idan aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe.
Komai na iya faruwa
Hakan kuwa yana nufin akwai yiwuwar sake tsunduma cikin yaki ko kuma tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar da ke aiki yanzu haka.
Tun ranar 7 ga watan Afrilu ne dai aka ayyana yarjejeniyar tsagaita wutar sakamakon shiga tsakanin da Fira Minista Shehbaz Sharif da Babban Hafsan Dakarun Tsaro Asim Munir na Pakistan suka yi don ganin an kawo karshen yakin.
Wasu manzarta dai na ganin za iyi wuya Trump ya aiwatar da barzanar ganin cewa a baya ma ya sha yin barazana kuma bai aiwatar ba.
