Kwamitin Amintattu na kungiyar tuntuba ta dattawan Arewa (ACF) ya yi watsi da dakatarwar da aka yiwa shugabancin sa karkashin Alhaji Bashir M. Dalhatu.

Majalisar Zartarwa ta Kungiyar Tuntuba ta Dattawan Arewa (ACF) ta dakatar da Shugaban Kwamitin Amintattu na kungiyar, Alhaji Bashir M. Dalhatu, bisa zargin rashin gaskiya wajen sarrafa kudade da kuma karya ka’idojin kundin tsarin mulkinta.

Jaridar Blueprint ta ruwaito cewa wannan mataki na zuwa ne a matsayin martani ga rikicin shugabanci da ya dabaibaye kungiyar a kwanakin nan.

Majalisar Zartaswar ta dauki wannan mataki ne yayin wani taro da ta gudanar a wani wuri na daban a Kaduna ranar Laraba, bayan da ’yan sanda suka hana mambobin shiga sakatariyar kungiyar dake kan titin Sakkwato.

Sakataren yada labarai na Kungiyar Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ya bayyana wa manema labarai cewa wakilai daga jihohin Arewa 18 da kuma Yankin Birnin Tarayya ne  suka halarci taron.

A cewar Farfesa Muhammad-Baba, majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan duba rahoton Kwamitin Da’a da Ladabtarwa wanda aka kafa domin bincikar korafe-korafen da aka shigar kan yadda ake sarrafa kudaden kungiyar.

Manyan matakan da aka dauka sun hada da dakatar da Alhaji Bashir M. Dalhatu daga mukaminsa nan take, bayan majalisar ta nuna rashin amincewa da shugabancinsa.

Sannan Majalisar ta bayar da umarnin gudanar da bincike na musamman kan duk wata harka ta kudi a kungiyar, ciki har da kudaden tallafin da aka tara mata bara, tare da umarnin dawo da duk kudin da aka gano an yi sama da fadi da su.

Game da matakin garkame ofishinta, Majalisar ta yi tir da matakin da ’yan sanda suka dauka, inda ta bayyana hakan a matsayin tauye hakkin dan’Adam da katsalandan cikin harkokin kungiyar na cikin gida.

Majalisar ta kuma jaddada amincewarta ga Kwamitin Gudanarwa karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar Barista Mamman Mike Osuman da tabbatar da dorewar Sakatare Janar na kungiyar a kan mukaminsa har sai lokacin da aka kammala duba kundin tsarin mulki.

Wannan mataki ya nuna yadda rikicin cikin gida na kungiyar ACF ya kazance, musamman kan batun gado da kuma ikon gudanar da mulki a tsakanin manyan kusoshin kungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *