Majalisar dokokin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), ta bayar da umarnin gudanar da bincike na hukuma game da karuwar hare-haren kyamar baki da ake kai wa baki ’yan Afirka a kasar Afirka ta Kudu.
Majalisar ta yanke wannan shawara ne yayin zaman farko na majalisar ECOWAS na shekarar 2026 da aka gudanar ranar Talata a Abuja, biyo bayan wani kudiri na gaggawa da dan majalisa daga kasar Ghana, kuma mataimakin shugaban majalisar na uku, Alexander Afenyo-Markin ya gabatar.
Yan majalisar sun amince da bai wa kwamitin ta na harkokin siyasa umarnin bincikar abubuwan da suka faru kwanan nan, na hare-haren nuna kyamar baki da suka shafi ’yan kasashen ECOWAS a Afirka ta Kudu.
A cikin bayaninsa, Afenyo-Markin ya bukaci shugabannin yankin da su fuskanci kalubalen tsaro da ’yan Afirka ta Yamma ke fuskanta a cikin gida da kuma kasashen waje.
Ya yi nuni da cewa tashe-tashen hankulan da ke faruwa kwanakin nan a Afirka ta Kudu, a yankunan KwaZulu-Natal, Cape Town, da Pretoria, inda aka bayar da rahoton kashe baki, raba su da muhallansu, da kuma lalata sana’o’in ’yafi shafar ‘yan Najeriya, Ghana, Zimbabwe, da Habasha ne.
Dan Majalisar ya yi kira da a dauki kwararan matakai na diflomasiyya da na shari’a, ciki har da tattaunawa ta hukuma da hukumomin Afirka ta Kudu da kuma hukumomin kare hakkin bil’adama na shiyya, domin tabbatar da an hukunta wadanda ke da hannu da kuma kare baki ‘yan gudun hijira.
Afenyo-Markin ya soki abin da ya bayyana a matsayin gibin dake tsakanin yarjejeniyar ECOWAS, na rashin walwala da muzgunawa a kan iyakoki da rashin tsaro a hanyoyi na kawo cikas ga kokarin dunkulewar yankin.
Bayan kammala tattaunawa, majalisar ECOWAS ta yanke shawarar aika wasiku ga majalisar dokokin Afirka ta Kudu, da kuma hukumar kare hakkin dan Adam ta Afirka, inda ta bukaci a gaggauta gudanar da bincike da kuma hukunta duk wani wanda aka samu da laifi.
Dubban yan kasar Afirka ta Kudu ne ke cigaba da fitowa kan titunan biranen suna bayyana rashin gamsuwa da yadda suke cewa yan kasashen waje na mamaye musu guraben aiki, tare da kiran cewar kowa ya koma kasar sa.
