Iyayen yara dalibai 42 da ‘yan ta’adda suka sace daga Makarantar Firamare da Karami Sakandaren ta Mussa a Ƙaramar Hukumar Askira/Uba ta Jihar Borno, sun ce har yanzu ba su san hali da kuma inda yaransu suke ba.
An sace ɗaliban, da suka haɗa da yara ƙanana masu shekaru biyu, daga cikin ajujuwansu a ranar 15 ga Mayu, 2026, lokacin da aka kai hari garin Mussa.
Babu wata ƙungiya da ta dauki alhakin sacewar ko ta tuntubi iyalai don neman kuɗin fansa tun bayan faruwar lamarin.
-
Majalisa ta gaza wajen dakatar da Gwamnati kan yawaitar cin bashi – Sarki Sanusi
-
Matatar Ɗangote ta fara shigo da ɗanyen mai daga UAE
Wasu daga cikin iyayen yayin zantawa da jaridar Daily Trust a ranar Lahadi, sun bayyana takaicin su kan abin da suka kira jinkiri daga hukumomin gwamnati kan sanar da su kokarin ceto yaran su.
Ɗaya daga cikin iyayen, Saleh Buba, wanda aka sace masa yara biyu ya ce “Muna tunanin yaranmu kowace rana saboda wasu daga cikinsu kanana ne. Daya daga cikin ‘ya’yana yana da shekaru biyu kawai. Ni da matata da sauran uwayen ba mu iya bacci ba tun lokacin da aka dauke su,”
Wata uwa, Josphin Yohanna, wacce aka sace ‘yarta mai shekaru uku, ta ce “Tsawon kwanaki 47, ba mu ji komai ba. Ba mu san ko yaranmu suna rashin lafiya, suna da lafiya, sun mutu ko suna raye ba.
Jami’ai sun ce mu yi hakuri saboda ana kokari, amma har yaushe za mu ci gaba da jira ba tare da wani labari ba?”