Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya zargi Majalisar Dokokin Tarayya ta ƙasa da gazawa wajen aiki da ƙundin mulkin ƙasa don dakatar da Gwamnatin Tarayya daga yawan cin bashi daga Babban Bankin Najeriya CBN.
Da yake magana kan bukatar samun ƙarin ƙarfi ga cibiyoyi da kuma tabbatar da riƙon amana a karshen makon da ya gabata, Tsohon Gwamnan CBN din ya ce akwai iyaka da doka ta tanada kan ciyo bashi da gwamnati za ta iya karba daga Babban Bankin.
Sarkin Kano ya bayyana cewa doka ta ba Gwamnatin Tarayya damar aron kuɗi daga CBN kaso biyar ne kawai na kuɗin shigar shekarar da ta gabata, inda ya yi zargin cewa ana karya wannan doka ba tare da majalisa ta ɗauki wani mataki ba.
-
FCCPC ga ’yan kasuwa: Ku sauƙaƙe farashin man fetur ko ku fuskanci takunkumi
-
Kwamandojin ISWAP 76 sun miƙa wuya ga sojojin Najeriya
“Dokar ta ce ba za ku iya ba da rancen da ya wuce kashi biyar na kuɗin shigar bara ba. An karya wannan dokar ba tare da daukar mataki ba.
Ina Majalisar Dokoki ta Kasa take? Na tsawon shekaru takwas, Majalisar ta yi shiru.”
“Ya kamata Majalisa ta yi dokoki kuma ta tabbatar ana bin waɗannan dokoki. Idan ba za ta iya tsayawa ga zartarwa ba, to ta zama wani ɓangare ne kawai na zartarwa maimakon zama bangare mai zaman kanta,” in ji Sarki Sanusi II.