Hukumar Kare Haƙƙokin Masu Saye ta Tarayya FCCPC, ta gargadi ’yan kasuwar man fetur da su daina cin zarafin al’umma, inada ta ce farashin fetur a kasuwa a yanzu ya saba da yadda farashin danyen man fetur na duniya ya faɗi.

Hukumar ta bayyana hakanne cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, inda ta buƙaci ‘yan kasuwan man fetur da su sauke farashin litar man.

Mataimakin Shugaban Zartarwa kuma Babban Jami’in FCCPC, Tunji Bello, ya ce duk da cewa Hukumar ba ta tsara yadda farashin fetur zai kasance to amma tana da alhakin kare mai saye daga cin zarafi da ayyuka marasa adalci.

“Muna damuwa da cewa yayin da masu siyarwa sukan ƙara farashin litar fetur idan farashin danyen man ya tashi, abin mamaki ne cewa yana ɗaukar lokaci mai tsawo kafin masu saye su amfana sosai idan farashin danyen man ya faɗi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *