Stephen Eustaquio ya zura ƙwallo mai ban sha’awa da ta baiwa kasar Canada nasara akan Afirka ta Kudu da ci 1-0 a wasan kofin duniya da suka fafata a Los Angeles.
Wannan ne karon farko da Canada ta tsallaka zuwa zagayen ƙasashe 16 a gasar kofin duniya.
Ƙasashen biyu sun baiwa juna wahala a filin wasa, yayinda masu tsaron gidan Afirka ta Kudu suka kare gidansu da gaske.
Sai dai kyaftin ɗin Canada ya raba gardama da wata ƙwallo mai tsafta da ya zura wadda ta baiwa Canada nasara a wasan.
-
DR Congo za ta ƙara da Ingila a zagayen ƙasashe 32 bayan ta doke Uzbekistan
-
Jordan 1-3 Argentina: Messi ya ƙara kafa sabon tarihi a gasar Kofin Duniya
‘Yan wasan Canada sun nuna ƙwazo sosai inda suka kai harin cin ƙwallo sau 12, yayinda Afirka ta Kudu ta kai hari sau 6.
Da wannan nasara a yanzu, ’yan wasan na Jesse Marsch za su fafata da Holand ko Moroko don gurbin wasan daf da na kusa da na karshe ranar Asabar mai zuwa.
