Yoane Wissa ya ci ƙwallaye biyu yayin da Jamhuriyar Dimoukraɗiyyar Congo ta farfado daga baya ta doke Uzbekistan da ci 3-1 a Atlanta, don tabbatar da fafatawa da Ingila a zagayen ƙasashe 32.
Ɗan wasan na Newcastle shi ne ya yi fice, inda ya zura ƙwallo ta biyu da ta uku a gasar don tabbatar da cewa ƙasarsa ta ƙare a matsayi na uku a Rukuni na K kuma ta samu nasarar farko a gasar Kofin Duniya.
- Jordan 1-3 Argentina: Messi ya ƙara kafa sabon tarihi a gasar Kofin Duniya
- Tawagar NFF ta halarci jana’izar tsohon kocin Najeriya, Onigbinde
Uzbekistan ce ta fara zura ƙwallo da wuri bayan fara wasa.
Da yake zantawa da manema labarai bayan tashi a wasan, Kocin DR Congo, Sebastien Desabre ya ce, “Dole ne mu yaba wa ’yan wasan – su ne suka yi abin ban mamaki.
“Mun kasance ƙasa da ta san yadda za ta farfado idan aka ci ta ƙwallo; za mu cigaba da gwagwarmaya cikin tsari.”