Sojojin Operation FANSAN YAMMA sun kashe wasu fitattun ‘yan ta’addan Lakurawa guda biyu tare da ƙwato makamai da alburusai a wani samame da suka kai a yankin Sabarumawa na Jihar Kebbi.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ya fitar, ya ce an gudanar da wannan samame ne a ranar 27 ga Yunin 2026 bayan samun sahihan bayanan sirri cewa ‘yan ta’addan na shirin kai hari kan al’ummar Sabarumawa.
Sanarwar ta bayyana cewa, bayan samun bayanan sirri, sojojin sun garzaya yankin inda suka yi kwanton ɓauna a hanyar da ake zargin ‘yan ta’addan za su bi domin dakile harin kafin ya faru.
- Me yasa aka karrama Ministan Yaɗa Labaran Najeriya?
- Kyaututtukan ƙanana da matsakaitan sana’o’i sun nuna ƙudirin Tinubu na bunƙasa tattalin arziki – Ministan Yaɗa Labarai
- ’Yan sanda sun kama wasu ’yan’uwa biyu kan zargin yi wa ƙaramar yarinya fyade
A cewar sanarwar, da isowar ‘yan ta’addan wurin, sojojin suka buɗe musu wuta mai, lamarin da ya haifar da musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu. A sakamakon haka, an kashe ‘yan ta’addan guda biyu, yayin da sauran suka tsere zuwa cikin dajin da ke kewaye da yankin.
Bayan kammala artabun, sojojin sun gudanar da bincike a yankin inda suka kwato bindigogi kirar AK-47, ƙwanson harsasai na AK-47, harsasai guda 143 da kuma babur guda ɗaya.
Rundunar ta ce wannan nasara na daga cikin ci gaba da ƙoƙarin da take yi na murƙushe ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka tare da tabbatar da tsaro a Jihohin Arewa maso Yamma.
Haka kuma, rundunar ta yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai cikin lokaci, domin ƙarfafa ayyukan yaƙi da ta’addanci da sauran manyan laifuka a yankin.