Karrama Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya biyo ƙoƙarin da yake ta fuskar wayar da kan al’umma game da yadda gwamnati ke aikin ta.

Bikin wanda aka shirya a ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa a ranar Asabar 27 ga watan Yuni, ya samu wakilcin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima.

Kyaututtukan da Minista Mohammed Idris ya samu sun haɗar da na kyautata Ƙanana da Matsakaitan Sana’o’i na Ƙasa na shekarar 2026, ƙarkashin tsarin (Renewed hope agenda)

Rawar da Ministan ke takawa wajen wayar da kan al’umma game da shirye-shiryen gwamnati na bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana’o’i sun kasance abubuwan da akayi la’akari dasu, wajen ƙarfafa masa gwiwar ɗorewa.

Har ila yau gudummuwar sa wajen fito da manufofin gwamnati ta fuskar bunƙasa harkokin kasuwanci da samar da ƙarin guraben ayyukan yi a faɗin ƙasar, na daga cikin abubuwan da masu shirya taron suka zayyano.

A baya bayan Minista Mohammed Idris, ya kasance akan gaba wajen ƙoƙarin wayar da kan al’ummar ƙasa a kafafen yaɗa labarai, game da manifofi da suka shafi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *