Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Nijeriya (JAMB) ta bayyIlimi daewa ana sa ran sama da mutum 300 za su halarci bikin karrama fitattun ɗalibai da za a gudanar nan ba da jimawa ba.
- Me yasa aka karrama Ministan Yaɗa Labaran Najeriya?
- Baiwa ƙananan ƴan kasuwa jari ke ɓunƙasa tattalin arziƙi-Mohammed Idris
A cewar hukumar, daga cikin waɗanda ake sa ran za su halarta akwai Ministan Ilimi da Magatakardan hukumar JAMB, Is-haq Oloyede da shugabannin jami’o’i da shugabannin hukumomin kula da ilimi da manyan jami’an manyan makarantu da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da abokan hulɗar da ci gaba da shugabannin kamfanoni da ɗalibai da kuma ‘yan jarida.
Hukumar ta ce haɗin gwiwar da ta ƙulla da kamfanin Rite Foods ya nuna ƙudirin ɓangarorin biyu na inganta ilimi, karrama gwaraza da masu ƙwazo, tare da ƙarfafa gwiwar matasan Nijeriya su himmatu wajen neman ilimi da samun nasara a karatunsu.