Sabon rahoto da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Human Rights Watch (HRW) ta fitar ya bayyana cewa dukkan ɓangarorin da ke rikici a ƙasar Mali na ci gaba da aikata laifukan take haƙƙin bil adama.

Rahoton ya zargi mayaƙan ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi, sojojin Mali da kuma dakarun haya na ƙasashen waje masu goyon bayan gwamnati da aikata manyan laifuffukan cin zarafin fararen hula tun bayan da rikicin ya ƙara tsananta a watan Afrilu.

A ranar 25 ga Afrilu, mayaƙan ƙungiyar JNIM mai alaƙa da Al-Qaeda, waɗanda ke ƙoƙarin hamɓarar da gwamnatin mulkin sojin Mali, sun haɗa kai da mayaƙan Azawad Liberation Front na Tuareg. A cewar rahoton, sun kashe Ministan Tsaron Mali, Sadio Camara, tare da ƙwace garin Kidal da ke arewacin ƙasar.

Rahoton ya kuma ce sojojin Mali da mayaƙan Russian Africa Corps sun mayar da martani ta hanyar kai hare-haren ramuwar gayya kan al’ummomin Fulani, tare da aiwatar da wasu hare-haren sama guda biyu da ake zargin sun kashe fararen hula.

A gefe guda kuma, mayaƙan JNIM sun kakaba wa babban birnin ƙasar, Bamako, takunkumin shiga da fita

A watan Mayu, sun ƙone motocin fararen hula sama da 40 da ke ƙoƙarin shiga birnin, sannan suka kashe wani mutum a bainar jama’a a garin Tonka, kusa da Timbuktu

Babban mai bincike kan yankin Sahel na Human Rights Watch ya ce ci gaba da rashin hukunta masu aikata irin waɗannan laifuffuka ne ke ƙara rura wutar cin zarafin fararen hula a Mali

Ya kuma yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) da Tarayyar Afirka (AU) da su goyi bayan gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano waɗanda ke da hannu take haƙƙin bil adama tare da gurfanar da su a gaban shari’a

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *