Tsohon ɗan wasan Barcelona, Robert Lewandowski, ya kusan canza sheƙa zuwa ƙungiyar Chicago Fire dake buga gasar Major League Soccer, ta kasar Amurka.

Lewandowski, ɗan asalin ƙasar Poland mai shekaru 37 ya bar ƙungiyar ta La Liga a ƙarshen kakar wasa bayan kwantaraginsa ya ƙare kuma ana sa ran zai sanya hannu kan kwantiragi na shekaru biyu a Chicago.

A watan Disambar da ya gabata, Chicago Fire ta ce sun yi magana da Lewandowski kan yiwuwar komawarsa ƙungiyar.

Lewandowski ya yi shekaru 12 a gasar Bundesliga ta Jamus tare da Borussia Dortmund da Bayern Munich, inda ya lashe kofin gasar sau 10 kuma ya jagoranci Bayern zuwa lashe gasar Zakarun Turai ta 2020.

An ɗauke shi a matsayin wanda ya fi kowa cancantar lashe Ballon d’Or na 2020 amma ba a bayar da kyautar ba a wannan shekarar saboda ɓarkewar annobar cutar Covid-19.

Ya zo na biyu a zaɓen Ballon d’Or a 2021, sannan ya lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan FIFA na Maza a 2020 da 2021.

Bayan ya koma Barcelona a 2022, ya taimaka musu sun lashe kofin La Liga sau uku da Copa del Rey na 2025, inda ya ci ƙwallaye 120 a wasanni 193 da ya buga wa ƙungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *