‘Yar wasan Birtaniya ta 1, Emma Raducanu ta janye daga gasar Wimbledon saboda Rauni da ta samu kwana daya kafin wasanta na farko.

An tsara za ta fafata da ‘yar ƙasar Croatia Antonia Ruzic a wasan farko na ranar Litinin a filin wasa na Court 1.

Raducanu ta rubuta a shafin sada zumunta ranar Lahadi da yamma cewa: “Ba zan iya yadda cewa hakan yana fitowa daga bakina amma cikin takaici na tilastawa kaina janyewa daga gasar Wimbledon na wannan shekarar.

“Na yi duk abinda zan iya don na kasance a filin wasa gobe amma bayan an yi min gwajin ƙarshe a yau da daddare, raunin da nake fama da shi ya ta’azzara, kuma likitoci sun ba ni shawarar na daina takurawa kaina.”

Ta ƙara da cewa: “Buga wasa a Wimbledon, a gaban masu goyon bayana daga gida, Babban abune gare ni, don haka ban samu lamarin da sauƙi ba.”

Raducanu, ta kwana biyu tana fama da rauni a kafar damarta tun bayan da ta kai wasan ƙarshe na Queen’s a farkon watan Yuni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *