Shugaban ƙungiyar Hezbollah, Naim Qassem, ya yi watsi da yarjejeniyar tsaro da Amurka ta shiga tsakanin Lebanon da Isra’ila, kwana guda bayan sanya hannu a kanta, yana mai bayyana ta a matsayin “mika wuya ga Isra’ila.”
A wani sabon lamari da ke nuna cewa rikici na ci gaba duk da yarjejeniyoyin tsagaita wuta da aka cimma a baya, Isra’ila ta kai hari ta amfani da jirgin sama maras matuƙi (drone) a kudancin Lebanon a ranar Asabar.
Sama da mutum miliyan ɗaya a Lebanon sun tsere daga gidajensu sakamakon rikicin da ya gudana tare da yaƙin Iran.
- Israila da Lebanon sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta
- Kenya ta tsaurara tsaro yayin da aka cika shekaru biyu da zanga-zangar matasan Gen Z
- Ana zargin cutar kwalara ta kashe mutum 24 a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka
Tsarin yarjejeniyar da aka cimma ranar Juma’a ya tanadi janyewar sojojin Isra’ila a matakai daga wasu yankunan kudancin Lebanon tare da tura sojojin Lebanon zuwa yankunan.
Sai dai kuma an amince Isra’ila ta ci gaba da kasancewa a yankin don faɗaɗa tsaro na wani lokaci.
A cikin wata sanarwa, Qassem ya bayyana yarjejeniyar a matsayin “mara inganci kuma babu amfani”, yana zargin gwamnatin Lebanon da yin rangwame ita kaɗai tare da tauye ikon ƙasar.
Ya kuma soki sharaɗin da ya danganta janyewar Isra’ila da kwance damarar Hezbollah, yana cewa hakan yana halatta ci gaba da zaman sojojin Isra’ila a Lebanon kuma ya wuce gona da iri.
Ya ƙara da cewa Hezbollah za ta ci gaba da gwagwarmaya, yana mai cewa “Ba mu bar fagen fama ba a lokacin mafi tsananin wahala, kuma ba za mu bar shi yanzu ba.
Tuni dai Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya nuna taswirar wasu yankuna biyu da ya ce Isra’ila za ta mika wa sojojin Lebanon nan gaba a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar.
Sai dai daya daga cikin yankunan ba ya cikin wuraren da sojojin Isra’ila suka mamaye, yayin da ɗayan kuma yake gefen sabon yankin da Isra’ila ta sanar da mamayesa a makon da ya gabata.